Advertising
Advertising
Labarai

Wasu ‘yan bindiga da ba’a san su ba sun harbe wata jarumar Fina-Finan Nallywood dake kudanci mai suna Ngozi Chiemeke

Wasu ‘yan bindiga da ba’a san ko suwaye ba sun harbe wata jarumar fina-finan Nollywood mai suna Ngozi Chiemeke dake kudancin Nageriya.

Advertising

Kamar yadda rahotanni bayyana cewa abin ya faru ne a titin Deeper Life a garin Boji-Boji Owa da ke Ƙaramar Hukumar Ika North-east ta Jihar Delta.

Mujallar Fim ta gano cewa an kashe jarumar mai tasowa ne a shagon ta na sana’ar hadahadar kuɗi na P.O.S.

Mutanen unguwar sun ce su dai sun ji tashin bindiga a wajajen shagon, to amma kafin su kai ɗauki har maharan sun arce daga wurin.

Advertising

An dauki gawar jaruma Ngozi Chiemeke an kai ta mutuware an aje kafin a yi mata jana’iza.
Kisan gillar ya haifar da babban ruɗani da baƙin ciki a garin, inda mutane su ka riƙa taruwa gungu-gungu su na tattaunawa a kai.

Jami’in yada labarai na rundunar ‘yan sanda ta jihar, DSP Bright Edafe, ya tabbatar da labarin kisan ga ‘yan jarida, ya ce, “Wasu maza da ba a san ko su wanene ba su ne su ka kashe matashiyar matar, amma an fara ƙoƙarin kama waɗanda su ka aikata wannan abu.

Mujallar Fim ta fahimci cewa wannan sabon kisan gillar ya faru ne ba da daɗewa ba bayan kisan da aka yi wa Cif Anthony Mkpado, wani ɗan kasuwa mamallakin shagon sayar da littattafai mai suna Mkpado Bookshop da ke kallon reshen bankin First Bank a garin na Boji-Boji Owa.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button