Mawaki Naziru M Ahmad wato sarkin waka ya bayyana wani al’amari game da shigar sa harkar Fim
Kamar yadda kuka sani Jaruma Nafisa Abdullahi ta fice daga shirin Labarina mai dogon zango wanda hakan ya janyo cece-kuce.
To bayan ta wallafa wannan labarin cewar ta fita daga shirin mai dogon zango Labarina, sai muka sami wata wallafa wanda Nazir M Ahmad wato Sarkin waka yayi akan cewa yayi dana sanin shiga harkar Fim.
Ga dai cikekkiyar wallafa a kasa.
Mawaƙin masanaantar Kannywood Naziru Ahmad wanda ake yiwa laƙabi da Sarkin waka, yash alwashin cewar daya san haka harkar fim take da bai shige ta.
Yana mai bayyana haka ne a wata tattaunawar sa da manema Labaru a babban birnin tarayya Abuja.
Yace gaskiya daya san haka harkar take da bai shigeta ba, yace rashin lokacin sanaar ne yake damun sa.
Shi ya saba tashi ne karfe 1pm na tsakiyar rana, yanzu kuma daya shiga harkar Fim karfe 9 ake fara daukar fim, kuma sai karfe 6 na yamma ake tashi, rashin lokacin bacci a harkar fim gaskiya yana takura shi.
Kazalika yace da alama dai yana ganin zai hakura da shirin fim kwata-kwata, zai cigaba da harkar sa da aka san shi da ita.