Bin shawarar Buhari ce ta sanya aka sami nasara a babban taron APC, cewar Gwamna Ganduje
Bin shawarar Buhari ce ta sanya aka sami nasara a babban taron APC, cewar Gwamna Ganduje
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano ya bayyana cewa, an samu nasarar gudanar da Babban Taron APC na Kasa cikin lumana da nasara sakamakon bin shawarwarin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar.
Ganduje ya fadi hakan ne cikin wata sanarwa da Babban Sakataren yada labaran Gwamna Ganduje Abba Anwar ya fitar a yau Lahadi.
Inda yace, yin aiki da shawarar Shugaba Buhari
yadda ya kamata shi ne yasa aka cimma nasarar data sa har aka sami sulhu tsakanin masu neman kujerar shugaban jam’iyyar ta APC.
Gwamna Ganduje yace, a wuraren da aka kasa samin sulhu shi ne aka yi zabe kamar yadda doka ta bukata.
Kamar yadda kuka gani an shiga zaben Kuma an kirga kuri’u an kuma bayyana wadanda suka yi nasara a zaben, inji shi.
Gwamna Ganduje ya yaba da cewa, a karshen taron an cimma abubuwa guda biyu cewa, mun fito da sabon salon shugabanci.
Na biyu kuma wannan taron ya sa muka kara
samun hadin kai da kara bunkasa kuma muna da tabbacin muna da nasara.
Rahoto daga Daily Nigerian Hausa.