Advertising
Advertising
Labarai

Innalillahi: Wata mata mai suna Aishatu Abubakar ta bayyana yadda ake Lalata dasu a wajan aiki a kasar Saudiyya

An tattauna da wata mata mai suna, Aishatu Abubakar, ‘yan garin Anka karamar hukumar jigar Zamfara inda a cikin tattaunawar da akayi da ita take bayyana cewa, ana daukar Mata da Maza domin zuwan wajan aikace-aikace da sunan kamfani amma sai ana lalata da matan.

Advertising

Da farko matar ta bayyanawa duniya sunanta da kuma abunuwan da suke faruwa a wajan wannan aiki da ake diban su ake kai su, inda take cewa sunan, Aishatu Abubakar, tana zaune a garin Ariyan.

Aishatu Abubakar ta bayyana cewa: Ana kawo musu fam domin su cike suje can wajan aikin da ake turasu amma ita tana kyautata zaton shi mutumin da yake kawo musu wannan fam din domin su cike suje wajan aikin bai san abin da ake aikatawa ba a wajan aikin, shi yasa yake kawo musu fam din domin su cike a matsayin ‘yan uwansa.

Zakuji yadda Aishatu Abubakar take bayani akan abubuwan dake faruwa a wajan wannan aikin da ake tura su wanda abin babu dadin ji, yadda ake lalata dasu a wajan aikin da suke zuwa duk zakuji a cikin bidiyon da take bayanin.

Advertising

Ga bidiyon nan domin ku kalla.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button