Labarai
Innalillahi wa inna ilaihi raji’un: Allah ya yiwa Sheikh Ahmad Bamba Kala Haddasana rasuwa
Allahu Akbar Duniya labari: yanzu yanzu muka sami labarin mutuwar ficaccan malamin addinin Musulinci dake Jihar Kano Sheikh Ahmad Bamba Kala Haddasana.
Advertising
Sheikh Ahmad Bamba Kala Haddasanaya rasu ne bayan gajeriyar rashin lafiya da yayi, kuma ya rasu ne a Asibitin koyarwa ta Malam Aminu Kano.
Iyalan Malamin sun sanar da cewa za a yi jana’izar malamin a Masallacin Darul Hadis da ke unguwar Tudun Yola a birnin Kano bayan Sallar Juma’a.
Fitaccen malamin ya yi fice ne a wajen karatuttukan Hadisi, inda a da can yake karantarwar a Masallacin BUK amma daga baya ya bude nasa wajen mai suna Darul Hadis.
Advertising
Advertising