Advertising
Advertising
Labarai

Yan ta’adda sun fara tuntubar iyalan fasinjojin jirgin kasa da su kai garkuwa da

Yan ta’adda da su ka kai hari kan jirgin kasa a kan hanyar sa ta zuwa Kaduna da ga Abuja a ranar Litinin sun fara tuntuɓar iyalan fasinjojin da su ka yi garkuwa da su.

Advertising

Iyalin wani da ga cikin fasinjojin da ya ke hannun yan ta’addan, mai suna Abdullahi, sun ce yan fashin dajin sun tuntube su ta wayar salula kuma sun ce musu su shirya biyan kudin fansa.

Jaridar Punch ta rawaito cewa: wani Jibreel Khalil, dan uwan Abdullahi d’in ya ce duk da ba su fadi nawa za a basu ba, amma dai yan ta’addan sun kira sun kuma ce yana hannun su sannan a shirya biyan kudaden fansa.

Ranar Litinin din data gabata ne wasu yan bindiga suka bude wuta a jirgin kasan dake tafiya daga Kaduna zuwa Abuja, inda wasu suka mutu da kuma wanda aka sace daga cikin harda wanda suka kira waya da zummar iyalansa su shirya biyan kudin dansa.

Advertising
Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button