Bayan dawowa da shirin Gidan Badamasi na Arewa24 an bayyana wani al’amari game da auren Junaidiyya da Alhaji Badamasi
Kamar yadda kuka sani an tsaya da haska Gidan Badamasi mai dogon zango wanda “Tashar Arewa24” suke haskawa saka kamo wasu sabbin tsarika da za’a fitar.
To a wanna Alhamis din data gabata 6 ga watan February 2022 an dawo da haska shirin mai dogon zango wato “Gidan Badamasi”.
Shirin wanda a zagon baya aka karkere da batun kai ‘yayan gidan Alhaji Badamasi gidan gyaran hali a sakamakon almundahana da sukayi tareda zanbatarshi.
Inda shi kuwa Alhaji Badamasi ya bayyana kudurinshi na Auren wata santaleliyar yarinya wato Junaidiyya.
Bayan dawowa wannan zangon ne dai Alhaji Badamasi yayi tattali kafa da kafa zuwa gidansu Junaidiyya domin tattaunawa da iyayenta kan batun aurensu da kuma biyan miliyan kudade da tsohon saurayin Junaidiyya ya bukata wanda yace ya kashe mata ne ayayinda yake neman Aurenta.
Saidai a irin son kudi na Alhaji Badamasi yace wannan kudi sunyi mishi yawa, kuma yana tantama ko kudin ma sun kai haka ko kuma A’a.
Abun jira a gani dai shine ko Alhaji Badamasi zai biya wadannan kudade domin samun damar mallakar Junaidiyya a matsayin matarshi ta Aure. Lokaci ne kawai zai tabbatar.