Yadda Aka sallaci gawa 145 a cikin mutane da yan bindiga suka hallaka ana cikuma cigaba da nemo wasu.
An kidaya mutun 143 wanda aka sami gawarsu akai musu sallah wanda ake tunanin Bello Turji ne sukai durar miki a kauyen karamar Hukumar Bukkuyum ta Jihar Zamfara ranar Laraba suka hallaka mutane. garin.
idan masu bibiyar hausa daily news zasu iya tunawa yaran Bello Turji ne suka kai hari garin Sun kai harin ne lokacin da suke ko karin tserewa bayan jiragen yakin sojojin sama sun tarwatsasu a cikin dajin Fakai da ke Karamar Hukumar Shinkafi, inda suka ya da zango suka halaka mutanen.
A cewar mazauna garin sunce an sami gawarwakin mutane da dama wasu a cikin gonakin su domin a shammace su.
Mazaunin garin yace an gama tataro mutanen da aka samu ragowar wanda suka ji rauni kuma sunyi gudun hijira.
Yakara da cewa yan bindiga sun tafi da shanu kusan 2000 sun kuma kara da cewa a kalla mutun 250 ne suka rasa rayukansu a wanan hari.