Jaruman Masana’antar Kannywood sun bayyana A, A Zaura a matsayin Dan takarar su a shekarar 2023

Jaruman Masana’antar shirya Fina-Finan Hausa ta Kannywood sun bayyana goyon bayan su ga Abdulssalam Abdulkarim Zaura wanda aka fi sani da A, A Zaura, a matsayin dan takarar neman zaben Gwamnan Jihar Kamo a shekarar 2023.
T. Y Asaba wanda jagoran ‘yan Fin din ne shi ya bayyana hakan bayan da Jaruman Masana’antar Kannywood din suka karrama A, A Zaura a ranar Asabat.
Shaba ya bayyana cewa: Zaura shine dan takarar ‘Yan Masana’antar Kannywood a jam’iyar APC a zaben gwamna na shekarar 2023.
Sannan Yace: Sun dauki wannan mataki ne duba da irin hidimar da A, A Zaura ke yi wajen tallafawa talakawa a Jihar da ma wajen ta.
Bayan haka Ya kara da cewa: Zaura ya zamo zakaran gwajin dafi wajen taimakawa masu karamin karfi ko da ba ‘Yan jam’iyar APC ba a fadin Jihar.
Ya kuma ce duba da irin hidimomin da ya ke na taimakon masu Ć™aramin Ć™arfi da kuma irin nasarorin da ya samu a rayuwar sa, sun samu yakinin cewa idan ya hau kujerar gwamnan Jihar Kano zai yi sama da haka kuma zai tallafawa Masana’antar Kannywood.
A nashi jawabin, A, A Zaura ya gode musu a bisa lambar girma da su ka bashi, sannan ya nuna cewa ya kamata al’umma su fahimci ‘Yan Kannywood cewa su na fadakar da al’umma ne ta hanyar fina-finan su.