Advertising
Advertising
Labarai

An bayyana irin cututtukan da suke shafar ‘yam mata masu yin Bilicin a nashiyar Afirka

Mayukan bilitin sun fi kasuwa da kaso 75% sabida yadda ‘yam matan Najeriya suke tururuwar zuwa siyan su, wanda daga ‘yam matan Nageriya sai ‘yam matan Senegal ne suka fi kowanne ‘yam mata siyan mayukan da kaso 60% domin su koma fararen fata.

Advertising

Bayan nan an bayyana yadda binciken na CNN ya gudana kamar haka:

Abubuwan da mata suke amfani da su wurin sauya launin fatar nasu sun hada da mayuka, sabulai, allurai da sauran su, sannan kuma yin bilitin yana janyo matsaloli da dama a jikin dan adam wanda ciki akwai cutar daji wato (Cancer) wacce take lalata fatar jikin mutum.

Advertising

Kamar yadda jaridar labarunhausa ta ruwaito cewa, akwai alamomi da dama da ake gane mutum idan ya kasance mai bilicin, akwai bayyanar tabbai a gabobi jikin mutum kamar na hannu, guiwa da sauran su.

Masana sun dade su na nuna illolin da ke tafe da sauya launin fatar dan adam wanda ake kira da harkar bilitin.

Sannan kuma akwai dalilan da suke sa mutane suna shiga harkar ta yin Bilitin mai hadarin gaske, suka ko kuma kushe halitta musamman ga mutane masu duhun fata ya kan tunzurasu su fada yin Bilitin, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Advertising

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button