Advertising
Advertising
Labarai

Jami’an tsaro sun kama wani kwarto da ya hallaka mijin Matar da yake daduro da ita

Jami’an hulda da Jama’a na rundunar ‘Yan Sandan Jihar Abimbola Oyeyemi ya bayyana wanda aka kashe mai suna Emaka Umonko, Mijin wata Mata wanda ake zargin ta da yin soyayya da wani mai suna Daniel.

Advertising

Kamar yadda gidan Talabijin na Channel Tv ya ruwaito, Ya bayyana cewa, an kama wanda ake zargin biyo bayan kisan da ofishin Dpo Na Onipanu ya samu.

A cewar Kakakin ‘Yan Sandan, Marigayin ya dade yana zargin cewa Udoh yana alaka da Matarsa wanda daga nan ya tunkare shi, lamarin da ya kai ga kazamin fada tsakanin Mutanen Biyu.

Kamar yadda Sahara Report ta ruwaito cewa, a yayin da ake cigaba da gwabzawa wanda ake zargin wanda Direba Banae, ya fito da wuka sannan kuma ya yi amfani da ita wajen dabawa marigayin gaba da bayansa da kuma kirjin sa daga nan ne marigayin ya fadi.

Advertising

Sannan kuma wata sanarwa tace, tuni dai Dpo din ya tura Jami’an sa domin suka yadda lamarin ya faru da kuma kamo wanda ake zargin, wanda daga baya aka ajiye gawar sa a dakin ajiye gawa na babban Asibitin Ifo domin cigaba da bincike.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Ogun, Lanre Bankole, ya bayar da umarnin a mika wanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka da leken asiri na Jihar domin cigaba da binciken.

Inda aka bayyana cewa, za’a gurfanar da shi a gaban kotu da zarar an kammala binciken gawar.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button