Labarai

Jami’an tsaro sun kama Mutumin da ya kashe ‘Yayan sa Mata 3 ta hanyar yi musu mummunar azaba

Jami'an tsaro sun kama Mutumin da ya kashe 'Yayan sa Mata 3 ta hanyar yi musu mummunar azaba

Yanzu yanzu muka sami labatin wani mutumi wanda ya kashe ‘Yayan sa guda uku ta hanyarvsaka su a cikin firinji.

Kamar yadda shafin BBC suka ruwaito cewa.

Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen Jihar Enugu ta kama wani mutum mai mai suna Ifeanyi Amadikwa bisa zarginsa da kashe ƴaƴansa mata uku.

A wata sanarwa da rundunar ƴan sandan ta fitar, mutumin mai shekara 52 bayan ya kashe ƴaƴan nasa, sai ya saka su a cikin wata lalataccen firinji.

Binciken da ƴan sandan suka yi sun gano cewa mahaifiyar yaran ta je kasuwa da ɗansu namiji ɗaya kacal, amma bayan ta dawo sai ta nemi ƴaƴanta mata ta rasa.

Sai dai a yayin da take nemansu, sai mijin matar wanda shi ake zargi, sai ya yi ta abubuwan da suka ja hankalin matar wajen firinjin wanda ya dawo da shi daga shagonsa.

Bayan da matar ta duba da kyau, sai ta ga gawarwakinsu a cikin firinjin inda ta ga akwai alamun duka a jikinsu.

A halin yanzu ƴan sandan dai na ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin faruwar wannan lamari.

Muna rokon Allah ya rabamu da irin wannan mummunar ta’asar wanda a karshe zamuyi nadama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button