Mawaki Dauda Kahutu Rarara ya fito da motocin kamfanin sa domim daukar mutane kyauta sakamakon yajin aikin ‘yan adai-daita sahu
Mawaki Dauda Kahutu Rarara ya fito da motocin kamfanin sa domim daukar mutane kyauta sakamakon yajin aikin 'yan adai-daita sahu
Mawaki Dauda kahutu Rarara ya bada umarnin fito da Motocin kungiyar sa na wasan kwallon kafa domin su rika daukar Mutane kyauta, saka makon yajin aiki da masu a dai-dai ta sahu suka shiga a Jihar Kano.
Kamar yadda kadaura24 ta rawaito cewa, al’umma da dama suna ta faman tafiyar kasa sakamakon yajin aikin da ‘yan adai-daita sahu suka fara yi tun a ranar litinin din data gabata.
A cikin wani bidiyo da mawaki Dauda Kahutu Rarara ya wallafa a shafin kamfanin sa ya bayyana cewa, an fito da Motocin ne domin taimakawa al’umma sakamakon mawuyacin halin da suka shiga sabida yajin aikin yan adai-daita sahu.
A cewar Mawaki Raraar, An fito da Motocin ne domin su dauki mutane musamman dalibai da zasu tafi ko zasu koma gida, kuma kyauta ba tare da sun biya ko sisin kwabo ba.
Al’umma da dama dai suna wahala sosai sakamakon yajin aikin da ‘yan adai-daita sahu, wanda ya faru sakamakon rashin fahimtar data shiga tsakanin Hukumar Karota da ‘yan adai-daita sahu din.