An yankewa wani Fasto mai suna Zafar Bhatti dake Pakistan hukuncin kisa dalilin batancin da ya yi ga addinin Musulinci
An yankewa wani Fasto mai suna Zafar Bhatti dake Pakistan hukuncin kisa dalilin batancin da ya yi ga addinin Musulinci
A yanzu ne muka sami wani labari akan wani Fasto mai suna Zafar Bhatti dake kasar Pakistan inda aka yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya, akan batancin da ya yi ga addinin Musulinci.
Daga Madogara Labarunhausa: Labarin ya fara kamar haka.
Lahore, Pakistan – Wata kotun yankin da ke Rawalpindi da ke kasar Pakistan ta yanke wa wani fasto, Zafar Bhatti, mai shekaru 58 hukuncin kisa kan batanci kuma yana gidan kurkuku tun 2012.
An zargi shugaban da aika sakonnin kar ta kwana na zagin addini. An yanke wa Zafar Bhatti hukuncin daurin rai da rai a ranar 3 ga watan Mayun 2017 karkashin dokokin Penal Code na Pakistan kan wulakanta Annabi Muhammad da mahaifiyarsa.
Kafin kama shi a 2012, Fasto Zafar Bhatti ne ya kafa kungiyar taimako ga “Jesus World Mission” da ke Pakistan domin taimakon marasa karfi kuma ya na da coci a cikin gidansa.
Kamar yadda korafin da wani wanda ba a sani ba ya mika, ‘yan sanda sun damke Fasto Zafar Bhatti kan batanci. Bayan bincikar wayarsa, an gano cewa layin da aka yi amfani da shi wurin tura sakonni, ba a yi rijistarsa da sunansa ba.
Wata mata Musulma mai suna Ghazala Khan a kasar Pakistan ce mai layin da aka yi amfani da shi wurin tura sakon, kotun ta gurfanar da matar a watan Afirulun 2013 kuma an bada belin ta.
Daga ranar farko, Zafar Bhatti ya musanta aikata laifukan da aka zarginsa, shi ne dan gidan fursuna mafi dadewa a kurkuku mai laifin batanci kuma shi ne aka fara yankewa hukuncin kisa wanda kotun ta jaddada a ranar 3 ga watan Janairu.
Ilyas Samuel, wam]ni Kirista mai rajin kare hakkin Dan Adam a kasar Pakistan yayin nuna damuwarsa kan kisan rashin adalcin da yace za a yi wa Zafar Bhatti ya bayyana cewa.
Wannan labari ne maras dadi. Ina takaicin yadda ake yi amfani da dokar batanci yadda bata dace ba kuma hakan ya zama ruwan dare kuma makamin yakar mutane masu gaskiya.