Advertising
Advertising
Labarai

Wasu ‘yan bindiga akan babura sun kai mummunan hari wani yanki a Jihar Kaduna tare da yin garkuwa da mutane

Wasu 'yan bindiga sun sake kaiwa mummunan hari wani yanki a Jihar Kaduna tare da yin garkuwa da wasu mutane

Wasu ‘Yan Bindiga sun kai hari wani yanki a Jihar Kaduna inda suka kashe wani Mutumi sannan kuma suka sace Matar sa.

Advertising

Bayan haka rahotanni sun bayyana cewa, an sace mutane wanda sun haura goma 10 a unguwar da al’amarin ya faru.

Wasu ‘Yan Bindiga wanda kwannen su yana kan babur dauke da mutum biyu 2, sun kai hari wani yanki a Jihar Kaduna mai suna Gbagyi Villa a daren ranar litinin data gabata.

Yankin da ‘yan bindigar suka kai hari yana daidai da wajan matatar mai ta Jihar Kaduna, inda suka kashe mutun daya 1 sannan kuma suka yi garkuwa da matar sa tare da wasu mutanen.

Advertising

Sai dai wani mazaunin unguwar da ‘yan bindigar suka kai harin ya tabbatar da cewa, mutanen da suke kan baburan sun hada da wasu ‘yan bindiga da suka tsere daga yankin.

A cewar mutumin mazaunin unguwar: A lokacin da ‘yan bindigar suka shiga kauyen mutane suka gudu amma sai ga wani mutum daya 1 wanda yake kama da ‘yan Banga, ya tsaya yana kokarin yin waya da wani abu kamar wayar wakie talkie nan da nan sai ‘yan bindigar suka harbi mutumin a kai ya fadi ya mutu.

Mazaunin unguwar ya kara da cewa: Bayan matar mutumin da ‘yan bindigar suka yi gatkuwa da ita, sun hada da wasu mutane sama da goma 10 wanda suma mazauna unguwar ne.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button