Advertising
Advertising
Labarai

Subhanallahi Yadda wata budurwa ta gamu da tsautsayi yayin da take talla masa

Abubakar Dala ya bayyana illar talla da kuma labarta yadda wani abu ya faru da wata budurwa yarinya mai saida masa.

Advertising

Kaman yanda na taqaita managar a shafina nace talla ya zama bara zana ga ‘ya’ya mata yanzu, musanman masu sayar da abinci, gyaɗa, pure water, masa, kwakumeti, ƙwai, kuli kuli, dama rauran su.

Wasu iyayen suna sakawa ‘ya’ya mata talla ne saboda su nima abin da za su ci kuma su qara rufama Kansu asiri saboda babu yanda za suyi, amma ana samun wasu iyayen suna sakawa yaran su talla ne saboda son abin duniya alhalin Allah ya rufa masu asiri babu shakka wannan babban kuskure ne ga iyaye mata

Watarana kusan sau uku ina ganin ana zubar da “masa” a bayan gidan mu abin ya sha bani mamaki ina “tambayan” kai na shin wa yake wannan aikin? ya zubar da “masa” masu kyau alhalin bai lalace ba, sai wani lokaci nafito daga gida misalin karfe goma na safe sai nayi ido biyu da mai wannan aikin ashe wata ƴar talla ce idan aka bata talla sai ta zubar da shi, kuma ba qaraman yarinya bace budurwa ce take wannan aikin. sai na “tambaye ta” ko me dalili idan aka baki talla kina zubar da shi? sai tace ai wani Alhaji ne yana mini juye kullum idan nafito wurin sa nake zuwa sai ya min juye kuma yaqara bar mini “masan” shi yasa nake zubar da shi domin kuwa idan bai qare ba mamana sai tayi mini dukan tsiya, sai abin ya bani mamaki da tace wani Alhaji ne yake mata juye kullum

Da yawa iyaye mata suna kuskure ki baiwa yarinya talla kice kar ki yarda ki dawo da wani abu agidan nan sai ya qare wannan kuskure ne babba saboda wannan kalman yana iya sa yarinya ta faɗa sherrin zina saboda tana tsoron kar ta dawo da wani abu, tana iya bayar da kanta domin ta samu kuɗin da zata baiwa wace ta bata talla gudun kar ta sha dukan tsiya.

Advertising

Wani lokaci ina tunani ko ƴara da ake basu talla kaman ba iyayen su ba ne, ƴaƴan goyo ne, domin nata ƴaƴan suna makaranta suna karatu sabado ba za ta yarda nata ƴaƴan suyi talla ba amma ita za ta baiwa ƴaƴan wasu talla. yana da kyau kusawa ƴaƴan ku ido agidan goyo

Kuma kaman yanda na faɗa a baya wasu yaran agaban iyayen su Suke son duniya ne kawai

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button