Advertising
Advertising
Labarai

Gwamnan Jihar Kebbi Atiku Bagudu ya bawa kungiyar Izala gudunmawar Naira Miliyan 50M domin gina Jami’ar Musulinci a Jihar Jigawa

Gwamnan Jihar Kebbi Atiku Bagudu ya bawa kungiyar Izala gudunmawar Naira Miliyan 50M domin gina Jami'ar Musulinci a Jihar Jigawa

Advertising

Gwamnan jihar Kebbi Sanata Atiku Bagudu ya
bawa kungiyar Izala gudunmuwar Naira Miliyan
50 domin gina jami’ar musulunci a Jigawa.

Bayanin hakan ya fito ne daga shugaban JIBWIS
na kasa Sheikh Bala Lau a Iokacinda sukeje yi
masa godiya a fadar Gwamnati dake birnin
Kebbi.

Ga cikakkiyar sanarwar kamar haka “Wakilan
Izalah bisa jagorancin Shugaban kungiyar Jibwis
Nigeria na kasa Imam Sheikh (Dr) Abdullahi Bala
Lau, sun ziyarci gwamna Kebbi Sen, Abubakar
Atiku Bagudu, a fadar gidan Gwamnati dake
Birnin Kebbi.

Advertising

A cewarjagoran tawagar Shugaba Imam Bala
Iau, sun je gidan gwamnati ne domin nuna
godiya ga gwamnan kan samun zaman Iafiya da
ci gaban jihar tare da godewa gwamnan bisa
samun tallafin Naira Miliyan Hamsin
(N50,000,000.00) na tallafin da Gwamnatinsa ta
basuwa domin gina Jami’ar As-Salam Global
University Hadejia ajihar Jigawa.

Bugu da kari, ya sanar da Gwamnan jihar kan
yadda aka warware rikicin da ke faruwa a cikin
Shugabannin kungiyar na jihar Kebbi tare da
gabatar da sabbin Shugabannin jihar.

A Iokacin da yake mayar da nashi jawabin, Mai
Girma Gwamna Sen, Abubakar Atiku Bagudu,
yayi godiya ga Shugabannin a ziyarar da suka
kawo masa da Kuma yabawa Kungiyar ta JIBWIS na gudunmawa da kokarin da suke basuwa ga Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, GCFR da kuma jiharsa (ta Kebbi).

Gwamnan ya kara godiya ga wakilan akan addua’arsu da goyon bayan da suke basuwa‘ Kuma ya gabatar musu da yara guda 30 da Malami Daya Wadanda aka karbo na FGC Yauri ya nemi da suyi musu addu’a.

Gwamna Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya
jagoranci Sheikh Bala Lau da sauran
Shugabannin Izala zuwa dakin taro na Banquet dake gidan gwamnati, inda suka gudanar da
addu’o’i na musamman ga daliban da aka sako
da kuma malamin kwalejin gwamnatin tarayya
dake Birnin Yauri.

Shugaba Bala Iau bayan sun kammala ganawa
da Daliban da da Malami Daya, da yi musu
addu’a, ya yabawa Gwamnatin Jihar Kebbi
(Kebbi State Government of Nigeria) na kokarin
kubutar da wadannan Daliban.

Shugaba Sheikh Bala Iau, yayi matukar godiya da yabo ga Gwamna Sen, Abubakar Atiku Bagudu, cewa ya cika alkawalin da ya dauka na bada tallafin Miliyan Hamsin, ga Jami’ar As-Salam Global University Hadejia, A ranar da aka
kaddamar da ita.

Shugaban Izala ya bayar da shawarar gudanar
da taron tuntubarjuna tsakanin Gwamnoni da
malaman addini a Iokaci-Iokaci domin tuntuba
tare da Ialubo hanyoyin magance kalubalen da ake fuskanta da suka shafi tsaro, tattalin arziki,
shugabanci da siyasa.

Daga cikin Tawagar akwai Sakataren Izalah na
kasa Sheikh (Dr) Muhammad Kabir Haruna
Gombe.

Ya gabatar da takardar yabawa da godiya daga
Shugaban kungiyar Jibwis Nigeria Sheikh
Abdullahi Bala Iau zuwa ga Gwamna Sen,
Abubakar Atiku” Bagudu.

Daga cikin Tawagar Shugaba Bala Iau akwai:
Sheikh Abubakar Giro Argungu, Sheikh Alaramma Ahmad Suleiman Ibrahim
Kano da Sheikh Dr Ibrahim Jalo Jalingo
sauransu.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button