Labarai

Asirin wani Mutumi ya tonu yadda aka kama shi da laifin yiwa ‘yar Matar sa mai shekara uku fyade

Asirin wani Mutumi ya tonu yadda aka kama shi da laifin yiwa 'yar Matar sa mai shekara uku fyade

Shahararran marubucin nan “Datti Assalafy” ya wallafa wani labari mai cike da abin mamaki wanda al’umma suka yi matukar jimamin abin da ya faru a akan abin da ya rubuta, akan wani mutumi da ya yiwa ‘yar matar sa fyade, ga yadda cikekken labarin yake.

Wannan mutumi da kuke gani a hoto sunansa Ali Lawan yana da zama a Anguwar Doya dake cikin garin Kirfi a jihar Bauchi, ya auri wata mata a matsayin bazawara, tazo gidansa da karamar yarinya ‘yar shekara uku.

Kwanaki biyar da suka wuce, wato ranar Lahadi 9-1-2022 da misalin karfe 6 na yammaci, sai Ali Lawan ya bukaci matarsa ta kawo masa taburma zai kwantar da ‘yar matar nasa.

Bayan ta kawomasa taburma ya kwantar da yarinyar kuma matar ta bar gurin, zuwa wani lokaci da ta dawo sai ta tarar da ‘yarta cikin mawuyancin hali tana amai ta baki da hanci, da ta duba gaban yarinyar sai ta ga ya dagargaje yana ta zubar da jini.

Nan take matar ta garzaya ofishin ‘yan sanda na karamar hukumar Kirfi, ‘yan sanda suka zo suka kama mijinta Ali, an kai yarinyar ‘yar shekara uku zuwa Asibiti inda Likitoci suka tabbatar Ali ya yiwa yarinyar fyade.

Yanzu haka Ali yana sashin binciken manyan laifuka na rundinar ‘yan sandan jihar Bauchi wato State CIID, bayan kammala bincike za’a mikashi zuwa kotu.

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button