Cin Amanar tsaro ya munana a Sokoto Zamfara: Shin Me ya Hada Musa kamarawa Aminin Bello Turji da Gwamnatin zamfara da Sokoto
CIN AMANAR TSARO YA MUNANA A SOKOTO DA ZAMFARA. Daga Datti Assalafy.
Kama abokin Bello Turji wato Musa Kamarawa da ‘yan sandan STS sukayi ba karamar nasara bace babba, abubuwa suna ta fitowa fili, duk wanda bai saurari jawabin Musa Kamarawa ba don Allah aje a saurara da kyau, na saka bidiyon a YouTube channel dina. https://youtu.be/CV6yVgnJnQI.
Wannan da kuke gani a hoto tare da Maigirma
Gwamnan Sokoto shine Musa Kamarawa abokin Bello Turji, kunji dai duk bayanan da Musa yayi a lokacin da ‘yan sanda suke tuhumarsa, ya tabbatar wa duniya cewa shi babban maciyin amanartsaro ne, ya hada kai da Bello Turji yaci amanar al’umma kuma yaci amanar kansa.
To amma wanene Musa Kamarawa da kuma
tasirinsa?, Musa Kamarawa mutumin Sokoto ne, yana da alaka na jini da tsohon Gwamnan jihar Sokoto Bafarawa kamar yadda ya furta da bakinsa, Musa Kamarawa yaron Gwamnan Sokoto ne a yanzu. sannan kuma yana da alaka da Gwamnan Zamfara na yanzu, duka Gwamnonin sun bashi mukamin SA akan sha’anin tsaro.
Gwamnan Sokoto ya bashi mukamin SA hakanan Gwamnan Zamfara, sunyi amfani dashi sosai akan matsalar tsaron jihohin nan guda biyu alhali yana matsayin babba aminin shugaban ‘yan ta’adda na yankunan, watakila ba da sanin Gwamnonin ba, watakila kuma da saninsu. wannan ba wanda ya sani sai Allah.
Amma abinda ke akwai shine, a tambayoyin da ‘yan sanda suka yiwa Musa Kamarawa yayi bayanin cewa akwai wani abokinsa mai suna Daniel shi yake sayarwa su Bello Turji miyagun makamai, to zancen da nake muku yanzu haka har an bada belin Daniel,shima Musa Kamarawa ana hasashen manyan ‘yan siyasa na Sokoto zasu sa 3 bada belinsa.
Kuma a cikin bidiyon da ‘yan sanda sukayi hira da Musa Kamarawa ya ambaci wani abokinsa Hashimu Kamarawa yana aikin sayarwa su Bello Turji kakin sojoji da na ‘yan sanda da takalma, Musa yace lokacin da ‘yan sanda suka sa ya kira Hashimu, a lokacin Hashimu yana cikin barikin sojoji na jihar Sokoto, har ma wani babban soja ya karbi wayan yake tambayar Musa Kamarawa a ina yake, abin tambaya me ya kai ‘dan ta’adda barikin sojoji?.
Shin manyan barayi irin wadannan da sukaci amanar kasa sukaci amanar al’umma su wa ke sawa a bada belinsu imba ‘yan siyasa da wasu manyanjami’an tsaro da manyan Sarakuna ba?, idan hakane ashe duk ta’addancin da ake a Zamfara da Sokoto ajandace, watakila shiyasa Maigirma shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya zuba musu ido.
Akwai wani kwamitin tsaro da aka kafa a Zamfara karkashin jagorancin tsohon shugaban rundinar ‘yan sandan Nigeria IGP MD Abubakar (mai ritaya) domin ya hada rahoto akan ta’addancin dake faruwa a Zamfara, kwamitin ya gama aikinsa. an samu manyan sarakuna da ‘yan siyasa da hannu dumu-dumu a ta’addancin, amma an hana a saki sakamakon bincike na Kwamitin. abinda ya faru kenan a Sokoto, akwai
wani babban Basarake a Sokoto ya hana a fitar da sakamakon binciken ta’addancin dake faruwa.
Kuma duk wannan abinda yake faruwa ba akan komai bane sai kudi, ‘yan siyasa sunci amanar al’umma, Sarakuna da suke wakiltar Musulunci sunci amanar Musulunci, sunci amanar Musulmai duk akan abin duniya mai karewa, da alama addu’ah da AlQunuti sun fara tasiri, asirin azzalumai maciya amana zai cigaba
da tonuwa her a wayi gari sun rasa mafaka da ikon Allah.
Muna rokon Allah Ya warware rawanin duk wani Sarki.