Wani bawan Allah mai kaunar shugaba Buhari ya sanyawa jaririn sa suna Muhammad Buhari
Wani bawan Allah mai kaunar shugaba Buhari ya sanyawa jaririn sa suna Muhammad Buhari
Wani Mutumi mai suna Malam maiwada Dan Malam ya daba labarin wani bawan Allah daya sami haihuwa, sannan ya yiwa shugaban Kasa Muhammad Buhari takwara da Dan nasa.
Malam maiwada ya bayyana hakan ne a shafin sa na sada zumunta Facbook, inda al’umma suke ta tofa albarkacin bakin su tare da yiwa jaririn addu’a ta gari.
Kamar yadda Dan Malan Maiwada yake cewa, wani abokin sa ne ya turo masa da cewa matar sa ta haihu a ranar Laraba da ta wuce, amma ya sanyawa dan nasa suna Buhari.
Kamar yadda Mutumin yace’ kauna da soyayya shugaba Muhammad Buhari ce tasa ya sanyawa dan nasa wannan sunan na shugaba Buhari.
Ina kwana mai girma jagorana. Ubangiji ya azurta ni da iyalina da samun jariri namiji a ranar Laraba, 12 ga watan Junairu, 2022.”
“Kuma saboda irin kaunar da nake yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari, na sa wa jaririn sunansa, Muhammadu Buhari.
Mutumin ya wallafa wani wani dan gajeren rubutu a kasan hoton jaririn kamar haka.
A message from a very good friend:
Good Morning my Distinguished Leader. God in his infinite mercy has blessed me and my family with a Gift of Baby Boy on Wednesday 12th January, 2022 and for my love to President Muhammad Buharil named the Baby after him Muhammad Buhari both the Mother and the Baby are doing well.
Me:
Allah Ya raya mana Muhammad Buhari, Ya sa albarka
a rayuwar shi.
A very big Congratulations to the familyyggyg