Advertising
Advertising
Labarai

Wata Mata ta kashe kanta ta hanyar yiwa kanta yankan rago dalilin wani zazzafan ciwon hannu da tayi wato kankare

Wata Mata ta kashe kanta ta hanyar yiwa kanta yankan rago dalilin wani zazzafan ciwon hannu da tayi wato kankare

Subahanallah komai yayi zafi maganin sa Allah: Yanzu muka sami labarin wata Mata wanda ake zargin ita ta kashe kan ta ta hanyar yiwa kan ta yankan rago, a unguwar sheka dake karamar hukumar kumbotso.

Advertising

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta tabbatar da Mutuwar wata Mata wanda ake zargin ita ta kashe kan ta a unguwar sheka dake karamar hukumar Kumbotso.

‘Yan sandan sun bayyana cews: Matar ta kashe kanta ne ta hanyar amfani da wani fasasshen gilashin taga, inda ta yanka kanta bayan gartsa wa mahaifinta cizo sannan ta gutsire dan yatsanta da ke ciwo.

Kamar yadda wani dan uwan marigayiyar mai suna Muhammad Sanusi ya ce: Kafin ‘yar uwar tasu ta kashe kanta ta yi fama da ciwon yatsa wato karkare, wanda har sai da ta kai ga sun rufe ta a ɗaki na tsawon kwana biyar, sakamakon yadda ta koma tamkar mai taɓin hankali, kamar yadda BBC Hausa suka ruwaito.

Advertising

Dan uwan nata Ya kara da cewa: A ranar da suka bude ta ne ta fasa gilashin tagar dakin da aka rufe ta sannan ta yanka kanta a makogoro.

A shekarar 2021 an samu mutane sama da biyar da suka kashe kansu a Jihar Kano da ke Arewacin Najeriya, wanda wasu daga cikinsu aka alakanta kashe kan nasu da matsalar kwakwalwa.

Sannan kuma Na baya-bayan da aka samu shi ne na wani matashi da ya kashe kan sa ta hanyar yanke al’aurar sa.

Allah ka rufa mana asirin mu duniya da lashir, Ameen.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button