Labarai

‘Yan bindiga sunyi awon gaba da abokan ango bayan sunje daurin auren sa suna kan hanyar su ta dawowa gida

'Yan bindiga sunyi awon gaba da abokan ango bayan sunje daurin auren sa suna kan hanyar su ta dawowa gida

Yanzu muka sami labarin cewa wasu ‘yan bindiga wanda ba’a san ko suwaye ba sanye da kayan Sojoji a jikin su sun yi awon gaba da wasu mutane guda bakwai 7, hakan ya faru ne a lokacin da suke kan hanyar su ta zuwa Isara dake juhar Ogun daurin aure a dai-dai wata hanyar Lagos kafin a karasa Ibadan.

Mutanen da ‘yan bindigar suka yi awon gaba da su sunje ne daurin aure a garin Ibadan dake jihar Oyo a ranar Asabar data gabata, amma abin ya ritsa da su ne a lokacin da suke komawa gidan su dake Lagos a ranar Lahdi, wanda a lokacin ma motar su guda daya ta lalace a yayin da suke lafiya, kamar yadda jaridar Punch Metro ta ruwauto.

Daya daga cikin wadanda abin ya rutsa da su, Folaha Akinsola, wanda ya zanta da Wakilin Jaridar Punch a ranar Litinin, ya bayyana cewa suna kokarin jawo motar da ta baci zuwa bakin hanya kawai masu garkuwan suka far musu.

Folaha Akinsola ya kara da cewa: Mun halarci wani daurin aure ne a Ibadan ranar Asabar, bayan daurin auren muka nemi daki a wanan wuri na Isara Washegari da misalin karfe 5:30 na safe muka hau shirin komawa jihar Legas. Tafiyar ta mu ta kasance a cikin ayari motocin mu guda uku da suka hada da Toyota Corolla guda biyu da Toyota Camry daya.

Ni ina cikin Toyota Camry wacce ta ke a gaba sauran biyu suna bin mu a baya inda wata babbar mota ta sha gaban mu mukayi kokarin wuce ta. yayin da direbanmu ya wuce wannan motar, har mun dan yi tafiya mai nisa kafin nan mu ka fahimci cewar fa mun baro ‘yan uwan mu a baya.

Sai muka juya baya muka koma don mu neme su. Mun dan yi tafiya kadan sannan muka same su a gefen hanya kusa da Isara. Daya daga cikin masu tuka motar mai suna Shola, ya ce motarsa ta samu matsala.

Sai Muka yi dabaran yankan bel ɗin motarsa don muyi amfani da igiya wajen daure motar a jikin ta mu saboda mu samu saukin janta zuwa gaba sai kawai muka ga wasu mutane su huɗu dauke da makamai sun fito daga cikin daji sun yo kanmu.

Amma A cikin mutum bakwai da aka sace Akinsola ya bayyana cewa, an sako mutum uku, a inda masu garkuwan suka bukaci a biya su kudi kimanin N60m domin fansan sauran mutum hudun da ke tsare.

Inda ya kara da cewa: Masu garkuwa sun fito ne sanye da kakin sojoji, inda suka tasa keyan mu zuwa cikin daji. Sun fi Su hudu, sauran suna daji ne. Sai da suka ƙwace kayayyaki mu kafin suka sake wasu daga cikin mu.

Ina cikin mutanen da na yi sa’a aka sako ni inda suka ce mu je mu nemo kudi naira N15m Kudin fansan ko wani mutum daya daga cikin ‘yan uwan mu da suke tsare a hannun su.

Don haka za mu tara jimilar kudi N60m kenan, don haka ne muke neman taimako a wurin al’ummar Najeriya saboda masu garkuwan sun ce za su hallaka su idan ba a samo wadannan kudaden ba.

Bayan mun yi nasarar kubutowa daga hannunsu sai mu kai kokarin kira lambar 911. Muna kan hanyar komawa Ibadan sai muka ci karo da shingen wasu ’yan sandan, muka yi saurin kai musu rahoton lamarin. Amma sai suka nuna mana cewa lamarin ba huruminsu bane. Sai suka tura mu sashin ‘yan sanda na Isara.

Daga baya mun kai rahoton lamarin inda shugaban jami’in ‘yan sandan wanan shiyya ya tura ‘yan sanda kusan 25 zuwa wurin da lamarin ya faru. Masu garkuwan suna ta aiko da bidiyoyin barazana na abokan mu dake hannun su.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button