Advertising
Advertising
Labarai

Anyi yinkurin hallaka wani matashi da aka ce za’a saka a fim din Kwana Chasa wanda gidan talabijin din arewa24 ke haskawa.

Wannan Matashi ana zaraginsa da yaudarar Wani Matashi cewa zai sashi a shirin Kwana Chasa In wanda ba gaskiya bane.

Advertising

Daga karshe bayan karbewa matashin dubu 70 yayi yunkurin hallakashi Kamar yadda kakakin Rundar Yan Sandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya shaida.

Abubakar ya ce ya yaudare shi ya kai shi karamar hukumar Danbatta inda ya karbi kudin suka kwana a gidansa.Da gari ya waye sai ya yanke shawarar ya mayar da kudinsa ya koma gida.

Abubakar ya hada baki da abokinsa mai suna Abdullahi Yellow wanda ake kira da “Horor”, inda Abubakar ya yi amfani da wuka mai kaifi, ya kwace masa wayoyin hannu guda biyu (2) ya yi yunkurin tsaga makogwaronsa ya tura shi cikin wata rijiya mai zurfi. Da kyar ya tsallake shingen ya tsallake rijiya da baya tare da yanka a wuyansa ya garzaya ofishin ‘yan sanda na Danbatta.

Advertising

Ka kakin yace ana cigaba da gudanar da bincike da zahrar an kammala za’a turashi gaban alkhali dan girbar abinda ya aikata.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button