Advertising
Advertising
Labarai

Wata Amarya a Jamus ta hana babbar kawarta shiga wajan liyafar auten ta sabida tayi kwalliyar da tafi ta kyau

Wata Amarya dake Jamus ta kwace katin gayyatar auren ta daga wahan kawar ta sabida tayi kwalliyar data kece raini wanda tafi Amaryar kyau.

Advertising

Kawar Amaryar mai suna Alena Yildiz ta bayyana cewa: Amaryar tayi Mata rashin Mutunci sabida tayi shigar data dauki hankulan Jama’a wanda ita Amaryar bata yi ba, daliljn haka yasa taki barin ta ta shi wajan liyafar auren nata.

Alena Yildiz ta wallafa wannan bayanin ne a shafin ta na sada zumunta instagram inda take cewa, a cikin su shida 6 ne kawayen Amaryar amma ita kadai aka maida saniyar waye inda aka hana ta shiga wajan liyafar bikin.

Kamar yadda Alena Yildiz take cewa, ita da Amaryar kawaye ne na kud da kud sannan ita Amaryar ce ta zaba mata kayan da zata sanya da kan ta a bikin nata, amma daga baya tayi mata wannan wulakancin.

Advertising

Yildiz ta ce ‘kawar tawa taji tsoron nayi kyau sosai hankali zai karkata akaina.’ A cewarta duk sauran kawayen sun caba ado sosai da kaya na alfarma da kece raini amma duk bata da matsala dasu sai nawa.

Yildiz ta cigaba da cewa duk da haka nayi hotuna da shigar tawa. Tace nayi mamaki idan tasan kayan zasuyi mana kyau sosai mai yasa ta zabo mana su a matsayin anko ai da sai ta zabo munanan kaya muyi anko dashi.

Sai dai hakan bai yi wa kawar dadi ba inda a yanzu suka raba jiha domin tana ganin babu amfanin kawancen nasu “kenan babu amfanin kawancen”.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button