Yadda wata budirwa ta rungume jarumin kannywood abale ya jawo cece kuce.
Daya daga cikin jaruman kannywood Daddy Hikima Wanda akafi sani da Abale acikin Shirin fim din ADUNIYA acikin wani gajeran bidiyo inda akaga jarumin suna rawa shida wata budurwa agidan Gala Wanda hakan yabawa mutane mamaki.
Wannan rawar dai tabar baya da Kura domin acikin bidiyon rawar anga inda Budirwar tasaka hannunta ajikin jarumin tana shafashi tana wasu kalaman Soyayya masu ratsa zuciya agaban yan kallo.
Tun Bayan Fitar wannan bidiyon dai aketa cece kuce akansa a kafofin sada zumunta inda masoyan jarumin suka nuna rashin jindadinsu akan abinda yayi acikin bidiyon kamar yadda zaku gansa wasu kuma suke ganin wannan ba wani abu bane.
Ga video rawar da sukai da jarumin.
Mungode da bibiyar shafin mu kucigaba da kasancewa damu dan samun zafafan labarai.