Labaran Kannywood

Bayan korar Rahama Sadau daga Kannyood a wannan karon ta dawo Masana’antar da karfin ta domin haska wani sabon shirin ta

Bayan korar Rahama Sadau daga Kannyood a wannan karon ta dawo Masana'antar da karfin ta domin haska wani sabon shirin ta

Jaruma Rahama Sadau yana dogon lokaci ba’a ji duriyar ta ba a Masana’antar shirya Fina-Finan Hausa ta Kannywood ba, to a yanzu ta dawo da karfin ta inda ta hara daukar wani shiri mai dogin zango mai suna “Matar Aure”.

An daina jin duriyar Jarumar ne tun bayan balahirar data faru na hotunan ta da suka tada kura a shafukan sada zumunta har ta kai ga wani kafiri yayi batanci akan hoton, dalilin haka akayi cha akan jarumar daga karshe kungiyar Moppan ta bada sanarwar an kori jaruma Rahama Sadau daga Masana’antar.

Koda yake jaruma Rahama Sadau ta cigaba da fitowa a Fina-Finan Kudu wato Nallywood har ma ta tsallake ketare tayi Fim a Masana’antar shirya Fina-Finai ta Bollywood na India, amma ba’a sake ganin ta a wani Fim a Kannywood ba.

Hatta Fim din ta mai dogon zango na ‘Yar Minista wanda ake haskawa a Youtube ta dakatar da yin sa wanda wasu suke ganin hakan yana da alaka da waccan dakatarwar da aka yi mata ne.

Sai dai kwatsam aka tsinkayi jarumar tana daukar sabon shirin nata mai suna “Matar Aure” wanda hakan yake nuna jarumar ta dawo Masana’antar da karfin ta, walau waccan dakatarwar da aka mata bata yi tasiri ba ko kuma kunnen uwar shegu tayi duba a Youtube zata saka Fim din nata.

Kuma Youtube basai da alaka da wata kungiya ko hukuma me ke akwai zamuji zamu gani wai an binne tsohuwa da da rai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button