Advertising
Advertising
Labarai

Bayan kwana 46 da sace wata yarinya mai suna Hanifa antsinci gawarta a wani waje

Kamar yadda kuka sani har yanzu ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane suna cigaba da aikata barna, wanda hakan yasa har yanzu al’umma suna cikin wani hali.

Advertising

To a yanzu muka sami wani labarin yadda aka sace wata yarin ya mai suna hanifa, amma bayan kwanaki arba’in da shida 46 da sace yarinyar sai aka kashe ta.

Wannan labarin ya fito ne daga kafar sada zumunta ta Facebook daga wani ficaccan marubuci mai suna Abba Gwale, inda ya tabbatar da mutuwar Hanifa a shafin nasa.

Amma a yanzu majiyar “Hausaloaded” tayi waya da iyayan yarinyar inda suka tabbatar da mutuwar Hanifa bayan an tsinci gawarta tare da rauni a jikin ta.

Advertising

Yau kwana arba’in da shida da sace yarinyar Hanifa bayan ta dawo daga makaranta, a yanzu haka anyi mata jana’iza kamar yadda addinin musulinci ya tanadar.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button