Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Hukumar tace Fina-Finan hausa tayi biris da wasu wakoki da ‘yam matan hausawa suke rawar zubda mutunci dasu a TikTok

Hukumar tace Fina-Finan hausa tayi biris da wasu wakoki da 'yam matan hausawa suke rawar zubda mutunci dasu a TikTok

A ‘yan kwanakin nan an yi tajin yadda shugaban hukumar tace Fina-Finai yake bayanin yadda hukumar zata shimmatu wajan hukunta ko tace duk wani Fina-Fiani masu dogon zango, da ake haskawa a shafukan sada zumunta musamman ma Youtube.

Advertising

Amma wasu suna ganin kamar hakan ba mai yiyuwa bane duba da Fina-Finan da ake haskawa masu dogon zango ba’a iya Kano kadai ake yin su ba.

Idan ma hakan ta faru wasu na ganin hakan zai dakile masu karamin karfi ko, kuma dora nayi biyu bayan sun sami sahalewar gwamnatin tarayya su kuma nemi na jihohi.

Sai dai ba ana gizo ke sakar ba wani cin sabula bula da aka dade ana yiwa hukumar kuma aka gaza magancewa shine, batun hannu yasan na gida da ake zaton suna yi a harkar tun bayan da hukumar ta kama wasu da ‘yan Masana’antar da ake sun raba gari a siyasan ce.

Advertising

Amma kuma ba’a taba ganin sun yi irin wannan kamen ga wa’yan da ake ganin suna tsagin su ba.

Wanda irin haka ce ta faru a kwanakin nan wanda ake dambarwa da wani mashiryin shiri da yayi wani shiri wanda ake zargin zai iya gurbata tarbiyyar al’umma musamman matasa.

Wanda hukumar ta shiga farautar shi wanda hakan yayi dai-dai da shirin sakin wata waka da wani mawaki mai tashe ke shirin yi, wanda ita ma taci karo da tarbiyya bahaushe amma kuma ba’a ji ana shirin daukar wani mataki ko tsaftace kalaman da suka saba ka’ida ba dake cikin wakar.

Amma baza’a ce an aki layi a bidiyon wakar ba tun bata kai ga fitowa ba amma tun a baitukan cikin wakar duk wani bahaushe da yaji yasan sunci karo da tarbiyya, wanda tun a yanzu ‘yam matan hausawa a TikTok ke wata irin rawa ta fatsara da zibda kima a dalilin suna bin wakar suna tattaba sassan jikin su.

Amma zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuga irin rawar da ‘yam matan hausawa suke wajan bin wannan wakar.

Koda ganin wannan rawa da ‘yam matan hausawa suke kun san cewa kalaman wakar sun bada gudunmawar assasa wannan rawa ta tozarci, inda suke korafi akan wannan wakar domin suna ganin kamar mai wakar na da uwa a gindin murhu shi yasa ba’a ce uffan a kan ta ba.

Kafin wannan wakar anyi irin wannan korafin akan wasu wakoki na Rarara da ake zargin shi da cin zarafin manyan kasa, har da inda yake kuntuma ashariya ana kuma kalubalantar hukumar tace Fina-Finai da rashin daukar wanu mataki a kai.

Advertising

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button