Advertising
Advertising
Labaran Kannywood

Zainab Sambisa ta kama matashin da yake amfani da sunan ta a shafin Facebook yana wallafa abubuwan banza

Zainab Sambisa ta kama matashin da yake amfani da sunan ta a shafin Facebook yana wallafa abubuwan banza

Kamar yadda kuka sani akan sami mutanen da suke amfani da sunan jaruman kannywood a shafukan sada zumunta suna abin da bai dace ba.

Advertising

To a kwanakin nan ne aka sami wani matashi wanda yake amfani da sunan jaruma Zainab Sambisa yana wallafa abubuwan banza wanda zasu janyo a zagi jarumar.

Bayan jarumar ta sha fadin cewa a daina aikata irin wannan abunuwan da sunan ta a shafukan sada zumunta amma ba’a daina ba, to a wannan lokacin tayi nasarar kama matashin da yake amfani da sunan nata yana wallafa abubuwan da basu dace ba.

Jarumar ta wallafa wata bidiyo domin ta shaidawa al’umma cewa ba ita take amfani da wannan shafin sada zumuntar ba wanda ake aikata abubuwan banza da sunan ta.

Advertising

Wanda har bayyana wanda wanda yake amfani da sunan nata yana wallafa hotunan da sauran abubuwan da zasu iya janyo mata zagi da kuma cece-kuce.

Inda har take cewa, ita bata ki wani ya bude shafin sada zumunta da sunan ta ba amma kada yana wallafa abubuwan banza wanda hakan zai iya taba mata kimar ta, duba da yadda ita ba haka halin ta yake ba.

A cikin bidiyon zaku ga yadda jaruma Zainab Sambisa take nuna matashin da yake amfani da sunan nata a shafin sada zumunta na Facbook, yana wallafa abubuwan da zaku iya janyowa a zage ta.

Wanda tace matashin yayi bayani da kan sa domin al’umma su shaida ba ita take wallafa wadan nan abubuwan ba.

Domin kuga shida cews ba jatuma Zainab Sambisa ce take amfani da shafin sada zumuntar da ake wallafa abubuwan da basu dace ba kama daga hotuna da bidiyo da sauran su, sai ku kalli bidiyon dake kasa.

Ga bidiyon nan kai tsaye domin ku kalla.

https://youtu.be/ojzCe4NF3qI

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button