Advertising
Advertising
Labarai

Shugaban Kasa Buhari yayi magana akan kisan wulakancin da aka yiwa Hanifa a Jihar Kano

Shugaban Kasa Buhari yayi magana akan kisan wulakancin da aka yiwa Hanifa a Jihar Kano

Shugaban kasa Muhammad Buhari yayi magana akan wannan abin ibtila’in daya faru a Jihar Kano, wato na sace wata karamar yarinya mai suna Hanifa wanda aka kashe ta cikin rashin imani aka daddatsa naman ta aka zuba a buhu sannan aka he aka binne ta.

Advertising

Kuma malamin ta wanda aka bashi amanarta yake koya mata ilimi da tarbiyya da yadda zataci nasarar a rayuwar, to shi ne ya aikata wannan danyan aiki akan karamar yarinyar wacce gaba daya bata wuce shekara biyar da haihuwa ba.

To a yanzu kamar yadda kowa ya sani wannan mutumin yana hannun ‘yan sanda kuma ya amsa laifin da ake tuhumar sa da shi, na sace yarinyar da kuma kisan wulakancin daya yi mata.

Shugaban Kasar Nageriya Muhammad Buhari ya jinjinawa ‘Yan Sandar Jihar Kano game da gano wanda ake zargi da kashe Hanifa Abubakar mai shekara biyar, tare da mika ta’aziyar sa da iyayan yarinyar.

Advertising

Wata sanarwa da Garba Shehu mai magana da yawun shugaban kasar ya fitar a jiya juma’a tace, shugaba Muhammad Buhari yana fatan hakan zai sa ‘yan kasa su kara amincewa da ayyukan jami’an tsaro.

Shugaba Buhari tace, iyaye da ‘yan kasa su dinga bin sawun halin da Hanifa ta shiga suyi ta fatan za’a ceto ta a raye, ya kara da cewa aikin gamo mutanen da jami’an tsaro suka gudanar da yakai an gano gawarta abin a yaba ne, abu ne daya kamata mutane su kara yarda da mahukunta, kamar yadda aka bayyana a cikin sanarwar.

Idan aka sami irin wannan abin alfaharin sai mutane sun dinga yabon jami’an tsaro a cewar shugaba Buhari, sannan yayi addu’ar Allah yajikan Hanifa kuma ya baiwa iyayan ta hakuri game da bakin cikin rashin ta.

A ranar Alhamis ne aka samo gawar Hanifa bayan da malamin makarantar su ya sace ta a watan Disamba, sannan ya kashe ta tare da binne ta daya daga cikin gine-ginen makarantar.

Tuni dai mutumin ya amsa laifin sa a hannun ‘yan sanda sannan kuma gwamnatin Jihar Kano ta rufe makarantar.

Mun sami wannan labarin ne daga tashar “Kundin shahara” dake kan manhajar Youtube, zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin labarin a karance.

Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla kai tsaye.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button