Advertising
Advertising
Labarai

Ina taya Matata Janine murnar cika shekara 48 a Duniya da kuma farin cikin kasancewa tare da ita, cewar Sulaiman Isah

Sulaiman Isah matashin nan daya auri baturiya ya bayyana irin farin cikin da yake shiga a suna tare da matar sa Janine wato baturiyar, Sulajman ya bayyana farin cikin na sa ne a lokacin da gudanar da bikin zagayowar ranar haihuwar matar ta sa Janine.

Advertising

Sulaiman Isa wanda yake da shehara 24 dan asalin Jihar Kano ya wallafa wani rubutu a shafin sa na sada zumunta Facebook, inda yake taya matar sa mai suna Janine Sanchez Raimann murnar cika shekara 48 a duniya.

Sulaiman Isah ya bayyana hakan cikin farin ciki a shafin nasa na sada zumunta Facebook, sannan kuma ya wallafa kyawawan hotunan su shi da matar tasa wanda hakan yake nuna cewa suna jin dadin zaman takewar aure su.

Advertising

Sulaiman Isah ya wallafa rubutun ne cikin harshen turanci a ranar da Janine matar sa ta cika shekara 48 a duniya inda ya wallafa rubutun kamar haka.

Happy birthday to my phenomenal wife whose love brings me everlasting happiness. Sweetheart, I cherish every moment I get to spend with youw. I Love You.

Sulaima yake cewa: Ina taya matata murnar zagayowar ranar haihuwar ta wanda soyayyar ta ce take sani nishadi da farin ciki a ko da yaushe, Sweetheart ina alfaharin kasancewar mu tare.

Sannan kuma ya kara bayyanawa duniya cewa, matar sa daban take da sauran mata domin tayi musu zarra, kuma ya kara da cewa yana matukar sonta da kuma farin cikin kasancewar su tare.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button