Labarai

Mahaifin Hanifa ya bayyana halin kunci da damuwa da da suka shiga shi da mahaifiyar ta tun bayan da aka sace ta

Mahaifin Hanifa ya bayyana halin kunci da damuwa da da suka shiga shi da mahaifiyar ta tun bayan da aka sace ta

Yanzu-yanzu mun sami wani sautin murya daga shafin instagram na BBC Hausa inda muka ji muryar mahaifin Hanifa yarinyar da aka sace ta tsawon kwana 46, sannan kuma wanda ya sace tan ya sashe ta.

Munji muryar mahaifin Hanifa yana bayani kan cewa, an sace ‘yar tasa ne tun a watan Disamba amma wanda ya sace tan a lokacin bai bukaci a bashi komai ba, inda suka yi matar sa wato mahaifiyar Hanifa sako ta cikin wayar ta kan cewa sun sace ‘yar su.

Sannan mahafin nata ya kara da cewa, sai bayan wata daya sannan wanda ya sace tan ya yi magana, ya kara da cewa sun shiga tashin hankali domin mahaifiyar ta ma kusan kullum tana shan maganin asibiti shi kuma ko abinci ma baya iya ci baya iya barci.

Sabida rashin cin abincin ne ma yasa ya rame ita kuma mahaifiyar Hanifa tashiga wani hali wanda har asibiti ya dauke ta ya jaita domin a duba lafiyar ra, sabida ita ma bata cin abinci kullum sai dai kuka har tsawon kwana 48.

Sannan mahaifin Ganifa ya kara da cewa: Hanifa ce kadai ‘yar da Allah ya mallaka musu sanna yace bayan da aka sanar da su cewa an sace ‘yar tasu, mahaifiyar Hanifa ta shiga wani yanayi wanda har asibiti aka kai ta aka yi mata sikanin sannan aka borata akan magani.

Ya kara da cewa: A lokacin da aka dauko gawar ‘yar tasu Hanifa ya shiga cikin halin dimuwa wanda har sai da aka rike shi aka sa shi a cikin mota.

Sanna kuma yace Hanifa yarinya ce mai basira da hazaka fara’a domin duk mutanen unguwar sun shaida haka, haka kuma idan aka tambaye ta wa take so sai ta dinga cewa baban ta-baban ta-baban ta

Mahaifin Hanifa ya bayyana irin damuwar da suka shiga shi da matar sa mahafiyar Hanifa a cikin sautin muryar da muka ji wanda shafin instagrma na BBC Hausa suka wallafa.

Domin kuji sauran bayani dafa bakin mahafin Hanifa sai ku kalli bidiyon sautin muryar dake kasa, inda zaku yadda ake masa tambayoyi ta cikin wani satim murya shi kuma yana bayani.

Ga bidiyon sautin muryar nan a kasa domim ku saurara.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button