Labaran Kannywood

Mansurah Isah ta fashe da kuka tana rokon gwamnati tasa a rataye wanda ya kashe Hanifa a kasuwa gaban jama’a

Ina rokon gwamnati tasa ana kashewa wadannan mugayen mutanen ko ana rataye su a kasuwa gaban jama'a, cewar Mansurah Isah

Har yanzu dai mhtane basu daina tofa albarkacin bakin su ba tare da tofin alatsine akan mutunin da ya yiwa yarinyar nan Hanifa kisan gilla ta hanyar bata guda bayan ta mutu ya daddatsa ta ya binne ta a rami.

To a yanzu tsohuwar jarumar Masana’antar Kannywood Mansurah Isah ta wallafa wata bidiyo a shafin ta na sada zumunta Instagram, inda take kuka tana jajantawa iyayan Hanifa.

Bayan haka jarumar ta yiwa Hanifa addu’a Allah yaji kan ta ya gafar ta mata, Allah yasa bakin wahalar ta kenan.

Sannan Mansurah Isah tana rokar gwamnati akan wannan mummunar aika-aika da mutanen suke wanda ba’a musu wani tsatsauran hukunci, ko kuma a kai su kotu a ajiye su to yanzu tana rokon aan kashe su ko kuna ana rataye su a kasuwa gaban jama’a.

Ga bidiyon nan a kasa domin kuji sauran bayani daga bakin Mansurah Isah.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button