Labarai

Mutumin daya kashe Hanifa ya bayyana dalilin daya sa yayi garkuwa da ita daga karshe kuma ya hallaka ta

To bayani ya fara fitowa daga bakin mutumin daya kashe yarinyar nan Hanifa inda yake bayani a cikin wata bidiyo da muka samu daga tashar Youtuve mai suna “Top Hausa”.

A cikin bidiyon munga yadda ‘yan jaridu suka kewaye mutumin suna masa tambayoyi akan mai yasa ya aikata mummunan kisa ga yarinyar.

sai muka ji yaba bayanin cewa, da farko akwai wasu mutum biyu da ya tura su wajan yarinyar wato Hanifa domin su tafi da uta amma sai taki.

Sannan kuma nan take sai ta fara kuka to amma da yaga taki yarda ta bisu sannab kuma ga matsalolin dake kan sa sa ya yanke shawarar kwanda kawai yaje ya dauke ta da kan sa.

A lokacin da ‘yan jaridar suka cigaba da tambayar sa mutumin ya kara da cewa, matsalolin dake kan sa guda biyu ne na farko shine a makarantar da yake domin ana binsa bashin kudade Naira dubu 70,000 sa kuma Naira dubu 80,000.

Sannan kuma yace, hatta gidan da yake ciki ana bin sa bashi to shine ya fara tunanin yadda zai kawar da wadannan matsalolin dake kan sa, har ta kai ga ya sace yarinyar wato Hanifa.

Bayan haka ya kara da cewa, da farko ya nemi naira Miliyan shida (6,000,000) a waja iyayan yarinyar wanda dana yana tunanin dole sun san za’a tambaye su kudaden.

Sannan yace, dama yasan idan ya sace yarinyar wato Hanifa yana da tabbacin zai sami wadanan kudaden, domin basai yana yashan wahalan neman wasu yaran ba sabida su dalibai ne yawanci yasan iyayan su.

Zaku iya kallon bidiyon dake kasa wanda muka samo ta daga tashar “Top Hausa” dake kan manhajar Youtube, domin kuji sahuran bayani da mutumin yake a lokacin da ‘yan jarida suke masa tambayoyi.

Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla kai tsaye.

https://youtu.be/dux5ElBJixw

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button