Labaran Kannywood

Tsohon jarumin Kannywood Kabiru Na Kwango ya bayyana akan yadda suka gina Masana’antar Fina-Fina tun asali

Tsohon jarumin Kannywood Kabiru Na Kwango ya bayyana akan yadda suka gina Masana'antar tun asali

Kamar yadda kuka sani akwai tsofaffin jaruman Masana’antar Kannywood wanda tun asali da su aka kafa Masana’antar, kuma har kawo yanzu suna taka mushimmiyar rawa a Masana’antar duk da basa fitowa a shirin Fim sosai.

To a wannan karon tsohon jarumin Masana’antar “Kabiru Na Kwango” ya yi shira da gidan jaridar BBC Hausa a wannan shirin nasu na daga bakin mai ita, inda yake bayani akan yadda aka gina Masana’antar Kannywood tun asali.

Kabiru Na Kwango yake cewa: Masana’antar Kannywood ta Alqur’ani ce an gina tane akan Alqur’ani da sauran Littatafai da Hadisan Manzon Allah S.A.W, akan haka suna kafa ta akan haka suna gina ta ga sunan su da ‘yayan su abin da suke ke nan.

Bayan haka Kabiru Na Kwango ya bada rashihin rayuwar inda yake cewa, an haife shi ne a shekarar 1962 inda ya yi karatuba hannun mahaifin sa ya yi karatu a hannun Malam Habu Zazzan.

Kabiru Na Kwango ya fadi abubuwa da dama yadda ya kamata game da tarihin rayuwar sa a shirar da suka yi da BBC Hausa.

Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji sauran bayani daga bakin tsohon jarumin Masana’antar Kannywood “Kabiru Na Kwango”.

Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button