Advertising
Advertising
Labarai

Wami matashi ya kashe abokin sa ta dalilin musun kungiyar kwallon kafa Chelsea da Barcelona

Wami matashi ya kashe abokin sa ta dalilin musun kungiyar kwallon kafa

Kamad yadda kuka sani a yawancin matasa masu kallon kwallon kafa suna samin sabani da junan su dalilin basa goyon bayan kungiyar daya.

Advertising

To a wannan lokacin ne muka sami labarin cewa, wani matashi ya kashe abokin sa dalilin wani sabani da ya shiga tsakanin su musun kungiyar kwallon kafa.

An gurfanar da wani dan shekara 18 mai suna Idris Yusif, a gaban babbar kotun majistare ta jihar Katsina, a bisa tuhumar sa da kashe wani Saifullahi Abdullah, a kan musun kwallon kafa.

Kamar yadda labarunhausa suka ruwaito cewa: Saifullahi mai shekaru 28 ya mutu ne bayan musu da suka yi akan wacce kungiyar kwallon kafa ce tafi wata, tsakanin Chelsea da Barcelona, inda daga baya, wannan musu ya rikide ya koma fada a tsakanin su, a ranar 12 ga watan Disambar shekara ta 2021, cikin karamar hukumar Danja dake jihar Katsina.

Advertising

Mahaifin Saifullah ya kai rahoton faruwar lamarin zuwa ga ofishin ‘yan sanda na Danja a ranar 20 ga watan Disambar 2021.

An gurfanar da Yusuf a gaban kotun Majistare a ranar Litinin ana tuhumar sa da laifin kisan kai, a karkashin sashi na 190, karamin sashi na(1) kamar yadda kundin tsarin doka na (penal code) ya tanada.

Ga cikekken rohoton yadda yake.

A ranar 18 ga watan Disambar shekarar 2021, da misalin karfe 3:30 na yamma, Saifullahi Abdullah yayi musu da kai, Idris Yusuf, dan shekara 18. A unguwar Hayan Asibiti dake Danja.

Akan wacce kungiyar kwallon kafa ce tafi wata karfi da kuma nagarta tsakanin Chelsea da Barcelona wadanda suke a kungiyoyin wasannin nahiyar turai. Wanda a sakamakon haka abin ya rikide ya zama fada wanda shi Saifullahi ya fadi magashiyan.

Daga baya, aka garzaya da mamacin cibiyar kula da lafiya ta Danja (Danja comprehensive health centre ) aka kwantar da shi, inda daga baya kuma likita ya tabbatar da mutuwarsa.

Bayan sauraron Dan Sanda mai gabatar da kara “Fadile Dikko”, ankalin kotun ta dage karar zuwa ranar 7 ga watan Maris shekara ta 2022.

Sannan kuma ta daba umarnin a cigaba da tsare Yusuf wanda ya aikata kisan a gidan kaso har zuwa ranar da za’a cigaba da shari’ar.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button