Advertising
Advertising
Wakokin Hausa

An tsinci gawar wata budirwa ta haihu kuma ta mutu a gefen asibitin Murtala.

An sami gawar wata budirwa da ta haifi yarta mace ita kuma Allah yay mata rasuwa bayan ta haifi yarinyar.

Advertising

Wani mutum mai suna Salisu da gidansa ke kusa da gidan gajiyayu dake kano wanda ke kusa da Asibitin Murtala yace: ya fito daga gida ne da misalin karfe bakwai na safe, Inda yaga matar kusa da kofar gidansa dauke da katin Asibiti tana zaune tayi tagumi.

Mutumin yace yayiwa matar magana ne tace masa Asibitin Murtala tazo. Shikuma jin haka yaga matar a gala baice kuma dauke da ciki Hakan yasa yarakata Asibitin.

Mutumin yakara da cewa ya raka matar kuma har yasata a layin ganin likita shikuma ya tawo gida. Daga nan ne ya tafi kasuwa.

Advertising

A cewar mutumin ya dawo daga kasuwa ya kara ganin budirwar a kwance a kusa da kofar gidan kwance cikin jini tuni yay wa mata magana dake aiki a gidan gajiyayu domin su duba syga meke faruwa da budirwar. Anan ne akaga ashe haihuwa tayi kuma Allah yayi mata rasuwa amma yar da ranta.

An samin wayar salula a hanunta an kira Gidan su da suzo an kuma kira hukumar yansanda da mai unguwar unguwa.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button