Advertising
Advertising
Labarai

Babban sako zuwa ga masu tunanin aikata mummunan laifi, daga Datti Assalafy

Babban sako zuwa ga masu tunanin aikata mummunan laifi, daga Datti Assalafy

BABBAN SAKO ZUWA GA MASU TUNANIN
AIKATA MUMMUNAN LAIFI
.

Advertising

Wannan sakon yana da amfani sosai a garemu gaba daya, a daure a karanta har karshe.

Abdulmalik Malamin da ya yayi garkuwa da
Dalibarsa Hanifa ya kashe ta, bincike ya nuna
a tarihi ba’a taba samunsa ya aikata wani
babban laifi ba, shaidar da abokansa suka bayar akansa ya nuna mutumin kirki ne a zahiri, kuma ance yana da addini da taka tsantsan da rayuwa, hatta sakonnin da yake rubutawa a shafinsa na facebook sun nuna hakan.

Na kalli cikakken hiran da akayi dashi da ‘yan
jaridu, ya zubar da hawaye sosai, yayi nadama wacce ba zata amfaneshi ba, ya roki iyayen Hanifa su gafarta masa da kuma sauran al’umma, wannan alamace dake nuni da cewa watakila ba mutumin banza bane, kuma watakila wannan shine karo na farko da ya taba aikata mummunan laifi haka.

Advertising

Na saurari hiran da akayi da Mahaifin Hanifa, ya fadi yadda Abdulmalik ya fara tura masa sakon yayi garkuwa da ‘yarsa, ya fadi inda zaije ya dauki kayan yarinyar domin ya tabbatar shi yayi garkuwa da ita, sannan ya fadi inda zai je ya ajiye masa kudi duk a guri daya, wannan alamace mai girma data nuna.

Abdulmalik asali ba kwararren Kidnapper bane, bai da wayo a Kidnapping, domin asalin Kidnappers basa haka.

To amma me ya kai Abdulmalik ya aikata mafi munin laifi na ta’addanci haka?.

Abu na farko: Abdulmalik bai da masaniya
akan rayuwar nadama ga wadanda aka kama
sun aikata babban laifi na kisan kai.

Abu na biyu: Da wahala a wayi gari mutum ya
lalace har yayi tunanin aikata mummunan laifi irin wannan ba tare da sanadin haduwa da abokan banza ba.

Abu na uku: Son zuciya da kuma gasa irin na
abokai.

Abu na hudu: Rashin hakuri da rashin juriya a
kuncin rayuwa.

Abu na biyar: Mummunan kaddara (Muna rokon Allah Ya karemu daga mummunan
kaddara).

Abin takaici me yasa Abdulmalik ya daddatsa
gawar Hanifa baiwar Allah bayan ya kashe
ta?.

Haka yana faruwa, idan an kashe mutum, sai aka rasa hanyar da za’a fitar da gawarsa, to sai a datsa gawar a saka cikin leda k0 wani abu a fita da ita ta yanda ba za’a gane ba, haka aka yiwa Dan Jaridar Kasar Saudiyyah Jamal Kashoggi wanda yake yiwa kasashen yamma leken asirin Daular Musulunci, Yariman Saudiyyah ya tura jami’an sirri suke sameshi a Masaukinsa dake Turkiyyah suka kashe shi, suka datsa gawarsa suka saka a leda.

Abdulmalik yana da sana’a, tunda shine mamallakin makarantar da Hanifa take, hakan na nufin yana da rufin asiri, don haka imba buri da son zuciya da gasa ba to babu abinda zai sa ya je yayi garkuwa har ya aikata kisan kai saboda kudi, domin garkuwa da mutane ba dabi’arsa bane, bai iya ba, kadiyyar abinda ya faru ya tabbatar da hakan.

Na jima ina tunanin cewa inda zan zama wani
babba a Nigeria, zan kawo tsarin da za’a saka
wani subject a aji domin a karantar da Dalibai
tun daga matakin Primary har University abinda ya shafi tsoratarwa kan aikata miyagun laifuka da dokokinsu da abubuwan da suke biyo bayan wadanda aka kama da laifin aikata miyagun laifuka, saboda ina gani da idona kuma a gabana halin da hatta ‘yan Boko Haram da manyan Kidnappers suke shiga idan an kamasu.

Karantar da yara da matasa akan gujewa aikata miyagun laifuka yana da amfani sosai, kuma hakan zai taimaka wajen rage aikata laifuka, saboda da yawan mutanen da suke aikata laifi ba su san abinda zai faru da su idan an kamasu ba, bayan azaba da suke dandana, zasu gwammace da iyayensu basu haifesu sun 20 duniya ba.

Duk wanda kasani masoyinka ne tun daga kan iyayen da suka haifeka sai sun gujeka, sai sun maka tofin Allah tsine, matarka zata bukaci ka saketa nan take, ‘ya’yanka ba zasuyi alfahari da kai ba har abada, zaka tafi ka bar musu mummunan tarihi da zai shafi zuriyarka gaba daya, rashin sanin abinda zai biyo bayan aikata mummunan laifi yana daya daga cikin abinda yake ingiza masu raunin imani zuwa ga aikata miyagun laifuka, shiyasa naga ya dace a a karantar da Dalibai a aji.

Manzon Allah (SAW) Yace ku taimaki wanda yayi zalunci da wanda aka zalunta, wani Sahabi yayi tambaya yace ta ya kuma za’a taimaki wanda yayi zalunci? sai Manzon Allah (SAW) Ya bashi amsa da cewa a hukuntashi daidai da laifin da ya aikata, da hakane duniya zata zauna lafiya, shiyasa Allah Ya saukar da ayar Qur’ani cewa wanda ya cire idon wani a cire nasa, wanda ya cire kunnen wani a cire nasa, wanda ya kashe wani shima a kashe shi.

Adalci da taimakon da za’a yiwa Abdulmalik shine a dauki rayuwarsa, a bashi guba ya sha,
sannan a daddatsa gawarsa kamar yadda ya yiwa Hanifa, wannan shine an masa adalci, kuma an taimakeshi, watakila hakan ya zama
kaffara a gareshi ranar Hisabi tunda Musulmi ne.

Jarrabawa a rayuwa:

Ita rayuwa hakuri ake da ita, idan kana son ka
godewa Allah a cikin wannan rayuwar, sannan ka zauna lafiya cikin aminci to a kullun ka kasance mai duba wadanda kafisu rufin asiri da walwala, kar ka yadda ka dinga duba wadanda suka fika rufin asiri, hakan zai sa ka fara tunanin bin muguwar hanya domin ka tara abin duniya wanda daga karshe zakayi nadama marar amfani.

A cikin sha’anin Ubangiji Mahaliccin mu, yakan jarraba mu a rayuwa, watarana zaka wayi gari baka da k0 sisi, watarana kuma Allah Zai baka abinda baka taba tsammani ba, ba zamu taba tabbata cikin walwala ba kamar yadda ba zamu taba tabbata cikin kunci ba, wannan jarrabawa ne Allah (SWT) Ya ke mana a rayuwa, ya kamata duk wani Musulmi ya san da wannan, hakan zai
taimaka wajen yakar zuciyarmu idan ta kudurta mana aikata mummunan laifi.

Yaa Allah idan Ka hukunta mummunan kaddara zata samemu a rayuwa Allah Ka canza mana ita zuwa kyakkyawa, Allah Ka tsare mana imanin mu, Ka sa mu wanye da duniya lafiya.

Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button