Dr. Abdallah Gadon Kaya ya bukaci a daddatsa mutumin daya kashe Hanifa a gaban jama’a
Kamar yadda kuka sani malamai sun fara martani akan mutumin daya kashe ‘yar karamar yarinyar nan Hanifa mai shekara biyar a duniya.
To a yanzu ma ficaccan malamin addinin musulinci “Dr, Abdallah Gadon Kaya” ya bayyana a cikin wata bidiyo infa yake bayyana bacin ran sa ga mutumim daya yiwa Hanifa kisan wulakanci.
Malamin yace, kawai kwanda a futo da mutumim bainar jama’a shima a daddatsa shi kamar yadda ya yiwa Hanifa, shidin ban za shidin wa wannan abin da aka bari ana yi na kashe mutane ba’a daukan mataki shi yasa ake cigaba da kashe mutane.
Dr, Abdallah Gadon Kaya ya cigaba da cewa, gashi nan musifar da ake cikin kenan an sace wannan an kashe wannan aikin kenan ya zama a jarida an gama hayaniya an bar abin ya tafi
A cikin bidiyon wanda tashar “Tsakar gida” ta wallafa a manhajar Youtube Dr, Abdallah Gadon Kaya yayi bayani sosai kan mutanen da suke aikata mummunan kisa da ta’addanci a wannan lokacin.
Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji sauran bayanin da Dr, Abdallah Gadon Kaya yake akan mutanen da suke aikata kisan kai sannan kuma aki hukunta su, kamar irin su mutumin daya yiwa Hanifa kisan wulakanci.
Ga bidiyon nan a aka domin ku kalla kai tsaye.