Labarai

Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un: An yi wani babban rashi da ake neman taimakon addu’ar ‘yan uwa musulmai

Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un: An yi wani babban rashi da ake neman taimakon addu'ar 'yan uwa musulmai

Innalillahi wa inna ilaihi raji’un: Yanzu muka sami wani labarin rasuwar wata baiwar Allah wanda har abokin dan ta ya bayyana a cikin wata bidiyo yana neman tayin addu’a ga ‘yan uwa musulmai domin Allah ya yi Mata rahama.

Da farko mutumin ya fara da sallama irin ta addinin musulinci inda yake cewa, sunana Al’amin Ibrahim kuma neman alfarma nazo gare ku, Allah ya daraja dan adam kuma wanda yafi matsayi a wajan Allah shi ne wanda yai jin tsoron sa.

Mahaifiyar aminina ita ce Allah ya mata rasuwa a daren ranar Alhamis wato daren Juma’a kenan Allah ya karbi rayuwar ta kamar yadda Allah ya yi alkawarin cewa dukkan mai rai mamaci ne.

Don haka kowa lokacin sa yake jira to ita nata lokacin ne yazo muma kuma namu lokacin muke jira, makasudin wannan bidiyo da nayi na yi ne domin neman addu’ar bakunan ku masu albarka kuyi mana addu’ar Allah ya mata rahama Allah yaji kanta Allah ya yafe mata kurakuranta Allah ya haskaka kabarinta.

Kasancewar dukkan addu’o’in ku abubuwan wanda muke bukata domin bamu san wanda yafi daraja a wajan Allah ba, wata kila wani yana can wani wajan idan yayi addu’a sai Allah ya amsa.

To muma a matsayin mu na masu wannan shafi mai suna “Hausadailynews” muna rokon Allah yaji kanta ya gafar ta mata, Allah ya haskaka kabarin ta.

Mu kuma idan tamu tazo Allah yasa mucika da imani Ameen.

Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuga murumin da yake neman taimakon addu’a ga ‘yan uwa musulmai akan rasuwar mahaifiyar abokin sa.

Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button