Labarai

Mahaifiyar Hanifa yarinyar da aka mata kisan gilla ta bayyana wani al’amari a lokacin da aka nemi kufin fansar ‘yar su

Yanzu-yanzu an sami damar tattaunawa da mahaifiyar Hanifa yarinyar da aka mata kisan gilla bayan an sace ta.

A cikin wata bidiyo da muka samu daga shafin sada zumunta na instagram muji yadda mahaifiyar Hanifa take bayyana yadda kuka yi da mutumin daya sace ‘yar su wato Hanifa, a lokacin da yake bukatar su bashi kudin fan sa.

Mahaifiyar Hanifa ta fara da cewa, alokacin da mutumin ya turo mata sako ta cikin wayar ta yana bukatar subada wasu makudan kudade har naira Miliyan shida, amma sai ta sanar da shi cewa basu da wadannan kudaden amma zai iya musu ragi.

Tana kuka tana cewa wai akan ‘yar ta take neman ragi, to daga baya sai mutumin ya sake turo mata wani sako jan cewa, su bada Miliyan biyar amma zasu iya cirewa dubu dari ta abaya.

Haka ta cigaba da bayyana abin daya faru ga maname labarai a lokacin da mutumin ya nemi a bashi kudin fan sa.

Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuga yadda manema labarai suka ziyarci mahaifiyar Hanifa, domin ta basu labarin abin da ya faru a lokacin da mutumin ya nemi kudin fan sa akan ‘yar su.

Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button