Alhamdulillah: An fara zakulo mutanen da suka taimaka wajan sace Hanifa domin a kashe ta
Alhamdulillah: An fara zakulo mutanen da suka taimaka wajan sace Hanifa domin a kashe ta
Kamar yadda kuka sani har yanzu ana tsaka da tattauna magana akan mutumin da ya yiwa Hanifa kisan gilla tare da wadanda suka mara masa baya.
To a yanzu mun sami wani sautin murya inda muka ji ana tambayar wata mata wanda ake zargin akwai sa hannun ta a lokacin da aka sace Hanifa kafin a kashe ta.
Lokacin da ake tambayar matar ta fara da cewa, sunan ta Fatima Jibrin Musa tana shekara 26 inda takw zaune a tudun murtala, sannan tace mutumin daya kashe Hanifa yaje ya same ta ne yake fada mata cewa akwai yarinyar da za’a je a dauka.
Sannan yace mata da shi da mahaifiyar yarinyar yaya ne da kanwa wai baban yarinyar ne zai kara aure shine dalilin da yasa za’a dauke yarinyar yaga idan aka tambayi kudin fansa a wajan mahaifin yarinyar to bazai iya kara auren ba domin kudin ya riga ya tafi a kudin fansar yarinyar.
Sai tace masa to shike nan ta nuna kamar batasan komai ba kawai washe sai yazo yace mata to taje wajan sa dake dakata za’a nuna mata yarinyar ta tafi makaranta, lokacin da taje dakata bata ganshi ba sai wani abokin sa ta gani baki sai sukayi waya da shi suka shiga wani layi yace mata ga yarinyar nan har ma yakira yarinyar amma sai taki taje wajan su.
Daga nan suka juya suka tafi gida tun daga nan bata sake ganin sa ba sai bayan na ta haihu da wasu lokuta sannan yaje wahan ta yace dan Allah ta kwafe masa wani rubutu daga wata fefar zuwa wata nan take sai ta kwafemasa ta bashi.
Ta kara da cewa, batasan garkuwa za’a yi da yarinyar amma sai ta sami wasu wanda take ganin girman su ta sanar da su abin dake faruwa, sai suka fada mata cewa ta cire kan ta daga ciki ko kofar gidan su karya kara zuwa tunda garkuwa za’a yi da yarinyar ko kuma idan yaje ta kira su.
zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji cikekken bayani daga bakin matar.