Advertising
Advertising
Labarai

An sace wani yaro mai suna Yusuf kamar yadda aka sace Hanifa yarinyar da aka mata kisan gilla, daga Fauziyya D Sulaiman

An sace wani yaro mai suna Yusuf kamar yadda aka sace Hanifa yarinyar da aka mata kisan gilla, daga Fauziyya D Sulaiman

Kamar yadda kuka sani labarin mutuwar Hanifa yarinyar da aka yi garkuwa da ita daga baya kuma aka kashe ta ha hanyar bata guba bayan ta mutu aka daddatsa sassan jikinta aak binne ta a rami, labarin ya daga hankulan al’umma da dama wanda har takai ga kowa yana jimamin mutuwar Hanifa.

Advertising

Wanda yanzu haka dukkannin al’umma sun zuba ido suna jiran wani irin hukunci za’a yankewa mutumin da ya yiwa Hanifa mummunan kisa.

To a yau kuma mun sami wani labari daga shafin “Fauziyya D Sulaiman”, inda ta wallafa labarin an sace wani yaro mai suna Yusuf kamar yadda aka sace Hanifa.

Fauziyya D Sulaiman ta wallafa labarin kamar haka.

Advertising

An sace Yusuf kamar yadda aka sace Hanifa tun shekarar da ta gabata, makarantar islamiyya din su daya da Hanifa har yanzu babu labarin sa, ku tayamu yadawa ko Allah ya sa a gano inda yake.

Muna rokon Allah ya bayyana wannan yaro mai suna Yusuf Allah yasa ba hannun wadannan mugayen mutanen ya shiga ba.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button