Advertising
Advertising
Labarai

An sake kashe wata yarinya mai suna Asma’u a jihar kaduna bayan kisan gillar da aka yiwa Hanifa a jihar kano

An sake kashe wata yarinya mai suna Asma'u a jihar kaduna bayan kisan gillar da aka yiwa Hanifa a jihar kano

Bayan wani labari da muka kawo muku a dazu wanda Fauziyya D Sulaiman ta wallafa a shafin ta na sada zumunta kamar haka.

Advertising

An sace Yusif Kamar yadda aka sace Hanifa
tun shekarar data gabata, makarantar
Islamiyya din su daya da Hanifa, har yanzu
babu Iabarinsa, ku tayamu yadawa ko Allah
ya sa a gene inda ya ke.

To a yanzu kuma mun sami wani labari yadda aka kashe wata yarinya wacce itama shekarun ta basu wuce na hanifa ba, yarinyar da aka mata kisan gilla.

Tashar “Kundin shahara” dake kan manhajar Youtube sun wallafa labrin yarinyar da aka kashe kamar haka.

Advertising

A lokacin da ake tsaka da jimanin kisan wulakancin da akai wa Hanifa yar shekara a jihar Kano, sai kuma gashi an kara samun kisan wata karama; yarinyar yar shekara 8, ita kuma mai suna Asma’u a jihar Kaduna.

To wannan lamari dai gaskiya ya zama abin da ya zama tunda dai har kananan yara ma basu tsira ba, tabbas wannan rashin imanin ya wuce misali.

Ita dai Asma’u mai shekara takwas da haihuwa an kashe ta ne bayan kwana 42 da sace ta, bayan an karbi kudin fansa a wajan iyayan ta har naira Miliyan 3.

Kamar yadda ita Hanifa malamin makarantar su ne ya sace ta, ita kuma Asma’u ‘yar jihar Kaduna makwabcin su ne ya sace ta, wato a ranar 9 ga watan Disamba daya gabata.

Wato duk wadannan yara guda biyu Hanifa da Asma’u an sace su ne a watan daya gabata na Disamba, inda kuma dukkan su aka kashe su a wannan watan da muke ciki na Jaruware.

Baya ga wannan kuma a lokacin baya da aka sace wata yarinya a jihar Kano sai dai cikin ikon Allah ita basu kashe ta ba, inda zakuji bayanin da yarinyar tayi bayan Allah ya kubutar da ita.

Ga bidiyon nan domin ku kalla.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button