Advertising
Advertising
Labarai

Subahanallah: Jirgin kasa yayi rugu-rugu da wasu mutane a cikin motar siminti ta dangwate tare da adaidaita sahu

Subahanallah: Jirgin kasa yayi rugu-rugu da wasu mutane a cikin motar siminti ta dangwate tare da adaidaita sahu

Yanzu muka sami wani labari wanda ya sanya al’umma cikin tausayawa na wasu fasinjoji da suka rasa rayukan su a yayin da wani jirgin kasa ya murkushe tirelar siminti ta dangote da adaidaita sahu a jihar kano.

Advertising

Lamarin ya farune a kantitin obasanjo a cikin birnin jihar kano da misalin karfe shadaya 11:30 na safiyar yau din nan.

Wasu shaidun gani da ido wanda suke gudanar da sana’o’in su a wajan titin jirgin sun bayyana cewa, sun hango tirelar ta nufo layin dogo a yayin da shima jirgin ya keto a guje.

Sannan suka kara da cewa, sunyi kokarin su yiwa direban tirelan alamar jingin yana nufowa amma bai kula ba, inda ya ya sharo tirelar a guhe ba tare da sanin jirgin ya kawo kai ba.

Advertising

A lokacin da direban tirelar yake kokarin ketarewa layin dogo nan take jirgin yayi awun gaba da tirelar.

Sannan akwai wani mai adaidaita sahu wanda yake biye da tirelar shima gabadaya jirgin ya hada da du ya kwamishe, kamar yadda wani shidar gani da ido ya fada.

Bayan haka shaidun sun kara bayyana cewa, anyi gaggawar garzayawa da fasinjojin cikin tirelar asibiti, amma ana kyauta zaton direban tirelar ya tsari da ran sa.

Ga hotunan a kasa domin ku kalla.

Advertising

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button