Advertising
Advertising
Labarai

Tonon asiri: Yanzu matar mutumin daya kashe Hanifa ta bayyana wani sabon al’amari akan mijin nata

Tonon asiri: Yanzu matar mutumin daya kashe Hanifa ta bayyana wani sabon al'amari akan mijin nata

Yanzu yanzu muka sami wani sautin murya na matar mutumin daya kashe Hanifa inda ake mata wasu tambayoyi game da lokacin da mijin nata ya dauki Hanifa ya kaita gidan sa.

Advertising

Da farko an tambayi matar kan cewa maibebe alakarta da Abdulmalik sai ta bada amsa da cewa mijinta ne, yayin da aka sake tambayarta da cewa ance ya kai Hanifa gidan sa ta zauna har na tsawon sati biyu wanda har ya sanya mata guba a abinci taci.

Sai matar tasa tace, ba sati biyu Hanifa tayi a gidan su ba kwanan ta biyar kawai a gidan inda ya sanar da ita cewa, mahaifiyar Hanifa tana aiki ne a makarantar da yake amma ta sami aiki a saudia to amma suna abuja zasu sa hannu kafin su tafi.

Dalilin haka ne ta bashi Hanifa kafin suje su dawo sabida mahaifiyar Hanifan ta auri iyamuri ne kuma ya koma kirista sabida haka nata so tabar Hanifa a hannun shi, sabida idan tabar Hanifa a hannun shi bayan ta tafi zai iya maida ta kiristan shi yasa tace ya rike Hanifa kafin ta dawo.

Advertising

Haka dai matar mutumin wanda ya kashe Hanifa ta bayyana dukkan abin da ya faru a lokacin da mijin nata Abdulmalik ya kai Hanifa gidan sa.

Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji bayani daga bakin matar mutumin da ya kashe Hanifa.

Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla kai tsaye.

https://youtu.be/vXuwORPhPnE

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button