Allah Sarki: Wani mawaki ya rare waka mai ban tausayi akan kisan gillar da aka yiwa Hanifa
Allah Sarki: Wani mawaki ya rare waka mai ban tausayi akan kisan gillar da aka yiwa Hanifa
Allah sarki duniya kenan, ita marigayiya Hanifa tata ta kare sai dai muce Allah yaji kanta ya gafarta mata yada bakin wagalar data sha kenan.
Marigayiya Hanifa ta sami dubban al’umma wanda suka yi mata addu’o’i da dama wajan nema mata rahamar Allah.
Wanda har yanzu al’umma basu daina jimamin mutuwar Hanifa ba duba da yadda yarinyar take da budadden baki da wayayyan kai, wanda har ma al’umma a yanzu suke jiran ganin wani irin hukunci za’a yiwa mutumin da yaci amanar iyayanta ta hanyar daukar ta daga makaranta yaje ya hallaka ta.
To a yanzu muka sami wata sabuwar waka wanda aka yi wa marigayiya Hanifa, wanda tashar Tsakar gida ta saki sabuwar wakar.
Wakar da aka yiwa marigayiya Hanifa ta dauki hankulan al’umma duba da yadda aka yi wakar tare da wa’azantar wa a ciki.
Zaku iya sauraran wakar da aka yiwa marigayiya Hanifa a cikin bidiyon dake kasa wanda tashar “Tsakar gida” ta wallafa.
Ga bbidiyon wakar nan a kasa domin ku saurara.