Advertising
Advertising
Labarai

Jaruma Zainab Sambisa ta shiga halin da za’a tausaya mata akan kisan gillar da aka yiwa Hanifa

Jaruma Zainab Sambisa ta shiga halin da za'a tausaya mata akan kisan gillar da aka yiwa Hanifa

Ficacciyar jarumar Masana’antar Kannywood Zainab Sambisa ta wallafa wata bidiyon a shafin ta na sada zumunta instagram, inda take kuka tana mai nuna bakin ta akan kisan rashin imanin da aka yiwa Hanifa.

Advertising

Jarumar ta bayyana a cikin bidiyon inda take fasge da kuka tana fadin cewa, dan Allah dan daraja da Manzon Allah S.A.W ‘yan Nageriya shuwagabannin mu da jami’an tsaro bamu raina kokarin ku ba, kokarim ku ne yasa har aka gano tsinannan mutumin da ya yiwa Hanifa kisan gilla.

To dan Allah yadda jami’an tsaro suka yi kokari akan gano shi dan Allah gwamnatin kasa ta Nageriya kudaukan mana kwakkwaran mataki akan irin wadannan mutanen, bamu san yadda zamuyi ba idan ana irin wannan tunda yauzu aka fara ba dama anayi.

Ta cigaba da cewa, amma kullum abin sai dai ya kare a kan mu mune bama posting.

Advertising

Jarumar tayi maganganu masu taba zuciya a cikin bidiyon data wallafa, inda take kuka tana cirewa irin mutanen da suke aikata rashin imani, irin na mutumin da ya kashe Hanifa ta hanyar bata guda sannan ya daddatsa ta ya binne ta a rami.

zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuji sauran bayani daga bakin jaruma Zainab Sambisa, akan kisan da aka yiwa Hanifa.

https://www.instagram.com/real_zainab_sambisa/tv/CZEX3yDIna1/?utm_medium=copy_link

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button