Advertising
Advertising
Labarai

Makwabcina ne yayi garkuwa da ‘yar ta Asama’u kuma ya kashe ta bayan mun biya kudin fansa, inji shu’aibu wa’alamu

Makwabcina ne yayi garkuwa da 'yar ta Asama'u kuma ya kashe ta bayan mun biya kudin fansa, inji shu'aibu wa'alamu

Yanzu yanzu muka sake cin karo da wani saban labarin shima wanda aka sace ‘yar wami mutumi mai suna Alhaji shu’aibu wa’alamu wamban dawaki.

Advertising

Kamar yadda Aminya ta ruwaito: Yarinyar mai shekara takwas 8 da haihuwa wanda ake zargin wani makwancin su ya hada baki da masu garkuwa da mutane inda suka kashe yarinyar, bayan sun karbi kudin fansa har naira Miliyan takwas.

Lamarin ya faru ne a birnin zariya dake jihar Kaduna inda aka wallafa labarin kamar haka.

Ana dai zargin makwancin Wa’alamu da kisan yarinyar mai suna Asama’u, bayan ya hada baki da masu garkuwa da mutane, inda suka kasheta bayan sun karbi kudin fansar nata.

Advertising

Mahaifin na Asama’u yace, tun a ranar tara ga watan Disamban aka sace ’yar tasa, kuma tun lokacin suka sanar da ’yan sanda tare da kai cikiya wurare daban-daban.

Sai dai ya mahaifin Asama’u ya kara da cewa, daga baya an fara kiran lambarsa inda aka bukataci ya biya naira Miliyan goma sha biyar 15 a matsayin kudin fansarta.

Sannan yace, daga baya mun basu naira Miliyan biyu bayan an kai musu kudin har unguwar Rigasa da ke Kaduna, sai suka ce sai an kara ba da Miliyan daya da dubu 45 kafin a sakota.

Ya kara da cewa, bayan mun biya kamar yadda suka bukata, sai kuma aka bugo mun waya a ranar Laraba 19 ga watan Janairun 2022 da safe cewa, sun kasheta daga nan sai aka kashe waya.

Alhaji Shu’aibu Wa’alamu yace, tun bayan sace yarinyar suna bin umurnin ne kawai gudun kada a hallakata amma sun riga sun gama sanin wanda ya saceta.

Mahaifin Asama’u yace, sun tabbatar da hakan ne sakamakon kwararan hujjojin da suke da su cewa, makwabcin nasa ne ya sace diyar tasa.

A yanzu haka dai jami’an ’yan sanda masu yaki da muggan laifuka na IRT suka kama wanda ake zargin domin fadada bincike.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button