Advertising
Advertising
Labarai

Sheikh Isah Ali Pantami yayi zazzafan martanin da yasa mutane zubda hawaye akan mutumin daya kashe Hanifa

Sheikh Isah Ali Pantami yayi zazzafan martanin da yasa mutane zubda hawaye akan mutumin daya kashe Hanifa

Ministan sadarwa Sheikh Isah Ali Pantami ya hori mahaifiyar Hanifa Abubakar yarinyar da malamin makarantar su ya mata kisan wulakanci.

Advertising

Sheikh Isah Ali Pantami ya yiwa mahaifiyar Hanifa nasiha ne a lokacin da ya kai ziyara gidan su domin yi musu ta’aziyya.

A lokacin da Pantami ya kai ziyarar ya yiwa mahaifin Hanifa malan Abubakar ta’aziyya sannan kuma mahaifin Hanifa ya dagorance Sheikh Pantami izuwa cikin gidan, domin yiwa mahaifiyar Hanifa tare da ‘yan uwanta ta’aziyya.

A lokacin Pantami yayi nasiha ga iyayan Hanifa akan wajibine suyi hakuri da irin wannan jarrabawar da Allah ya kawo musu mai tsanani.

Advertising

Baya haka Sheikh Pantami ya roki Allah ya sanya Hanifa ta zamo mai cewo a ranar lahira ga iyayan ta, sannan ya bawa iyayan Hanifa hakuri akan wannan babban rashi daya same su ta sanadiyya wasu azzaluman mutane da suka nuna rashin imanun su akan Hanifa.

Iyayan Hanifa sun mika godiyar su ga Sheikh Isah Ali Pantami akan ta’aziyyar da ya musu, sannan kuma sun masa addu’ar fatan alkairi akan nasihohin da addu’o’in da Sheikh Pantami ya gabatar a lokacin da yaje ta’aziyyar Hanifa.

Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla kai tsaye.

Advertising

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button